Zuma on the beat
BASH NEH PHA
BASH NEH PHA
BASH NEH PHA
Sauka na a acaba, naga yarinya da jan zani
Yarinya ce mai kyau irin wanda kasani
Kalanta na wuya, samun irinta wuyan gani
Dole maza su biki, dan baki ba bakin jini
Ta bude man ido cikinsu mintinan da ban gani
Ta harbe ni da kyau, ta ma zuciyana muntsini
Ina ma zai yiwu, raba hanta da gudan jini
Abunda kikayi man, kawai dole ne ma kin sani
Kina da kyau, kawai dole ne ma kin sani
Kallon ki da dadi (kamar film)
Jin ki da dadi (kamar waka)
Jin ki da dadi (kawai kin hadu)
Girl you are beautiful
Kin man shock mana, kin taba rai
Ko ki tsaya, ko kuma ki kashe rai
Ina so ki sanni, ko daga ina kika fito
Ina so ki sanni, ko bakya kula samari
Ba kya tuwo da gari
Mai kyau bugu da kari
Ina so ki sanni
Ina so ki sanni
BASH NEH PHA
Zuciya tana bugu daya-daya kaman agogo
Don kawai saboda kallonki har na gware da bango
Ga halitta ta daban, Allah sa ta kula dogo
Ko a littafu naga irinki, dole in yago
In rabu da ke gwanda inci attarugu mai yanho
In shiga hannun hukuma su kafe ni a bango
Ke kyau dai da natsuwa, jikinki aka wurgo
Ko ba ido ma dankali daban dashi da rogo
Dama ke nake ta nema kaman hulan Chicago
Kalan ki na wuya ko za'a zagaya a zago
Kin sani na natsu, kamar maciji a kogo
Tunanina zamu dace kaman tunkiya da rago
Kuma zai yi kyau da kallo, mune amarya da ango
Kin ga ni ina da sana'a kuma inada kango
In ma baki san bakanike in je in bude shago
Dan zaman mu ni da ke kaman da cigaba na hango
Tunda ni ina da jama'a har su Adamu Zango
Da mawaka da yan ball masu abota da tango
Kuma an sanni a lagos nan har garin jalingo
Dan mana, dan kauna sai in tsinko maki mango
Kallon ki da dadi (kamar film)
Jin ki da dadi (kamar waka)
Jin ki da dadi (kawai kin hadu)
Girl you are beautiful
Kin man shock mana, kin taba rai
Ko ki tsaya, ko kuma ki kashe rai
Ina so ki sanni, ko daga ina kika fito
Ina so ki sanni, ko bakya kula samari
Ba kya tuwo da gari
Mai kyau bugu da kari
Ina so ki sanni
Ina so ki sanni
Ina so ki sanni, kyau kin wuce gasa
Kuma na iya maganganu fiye da dan siyasa
Yauwa kina son cakulkulu? Ni na iya wasa
Kina so ki leka zuciya, ni zan baki ki lasa
Tsohuwar magana, ai garin masoyi babu nisa
Cikin garin kano inada 'yar uwa Nafisa
Zata miki farfedun kansa, kan sa mai kyau
Dariya ta fesa, tace saurayi
Kamar musha hannu mu gaisa
Samari su na ta so na, su na marmari a nesa
Kai kadai ka taba rai naji kamar na taka kusa
Tun tuni na so na amsa
Dole dai na kaika nesa
Ina son ka mai kalamai, ga kunnena ka fesa
Mai kyau ke zaki ya kisa
Kallon ki da dadi (kamar film)
Jin ki da dadi (kamar waka)
Jin ki da dadi (kawai kin hadu)
Girl you are beautiful
Kin man shock mana, kin taba rai
Ko ki tsaya, ko kuma ki kashe rai
Ina so ki sanni, ko daga ina kika fito
Ina so ki sanni, ko bakya kula samari
Ba kya tuwo da gari
Mai kyau bugu da kari
Ina so ki sanni
Ina so ki sanni
Kallon ki da dadi (kamar film)
Jin ki da dadi (kamar waka)
Jin ki da dadi (kawai kin hadu)
Girl you are beautiful
Kin man shock mana, kin taba rai
Ko ki tsaya, ko kuma ki kashe rai
Ina so ki sanni, ko daga ina kika fito
Ina so ki sanni, ko bakya kula samari
Ba kya tuwo da gari
Mai kyau bugu da kari
Ina so ki sanni
Ina so ki sanni
Zuma on the beat
Kawai kin hadu
Girl you are beautiful
Поcмотреть все песни артиста