In kayai fari Yace kayai fari In kayai baki Yace kayai baki In kayai kudi Yace kayai cuta Dan adam ba'a iya maka Komai zakayi Kai karka duba dan adam Don ko me kayi Shi sam ba'a iya mishi dan adam Don haka ko ya mutu Sai an daure dan adam Malam kayi aikin gaban ka Kar ka biye masa dan adam Ba'a iya masa Idan na dauki wasa Sai gwadan ya nake haka ne (Allah sarki gwanja) Idan na dauki gasken Sai su gwadan ai na yaudara ne (Manta dasu kawai) Tillas bidar uwa An iske dare ne ana dara Mai tsoro shi yake jira (Hakkun) Shi wazai kurbi kurkura Masoyi karka kuskura Domin in dai ka kuskura Wallahi komai ba'a iya maka Dan adam ba'a iya masa Dan adam ba'a iya masa Ko ya mutu sai an daure Dan adam Eh mana Dan adam ba'a iya masa Dan adam ba'a iya masa Me ne ke kai goma gidan tara Muje gwanja mu ta kirkira Yau da gobe sai munyi hatara Komai nisa muke jiran kira Gobara bata cin halaliya Mu raba kan mu Da cin haramiya Don muyi karko Mu mori duniya Allah shiga tsakanin mu Da yan iya Masu kuri masu fariya Masu karya masu karairaya Yadda Allah ka bamu duniya Sa da munje mu mori lahira Dan adam ba'a iya masa Dan adam ba'a iya masa Ko ya mutu sai an daure Dan adam ba'a iya masa Eh mana In anyi ruwa ya fadi anyi Sanyi ya fadi anyi Zafi akayo ya fadi anyi Da ka talauce yayai ta fadi kayi In kayi kiba ya fadi kayi Ka rame ma ya fadi kayi Dan adam shi ba'a iya masa Sai ran da yaji shi cikin kasa Malam kayi wa rawarka zamanka Kar ka biye masa Ba'a iya masa Dan adam ba'a iya masa Dan adam ba'a iya masa