Ku sha labarina Zance na jari na Adam me waka ne Naziru ban fada ba Labarina Inzo hira a tashi ban fada ba Labarina Masoyiya ki soni hagu da dama Labarina Idan kin ka fade shi ban musa ba In baki rai ashe gara ki soni ba kadan ba Labarina Inzo hira a tashi ban fada ba Labarina Masoyina ka soni hagu da dama Labarina Idan kai ka fade shi ban musa ba In baka rai ashe kaga ka soni ba kadan ba Masoyi mai ado da tufa mai kalar sarewa Masoyi mai kama da suga mai shigen kwalwa Masoyi mai issar da sani guna kafi kowa Masoyi mai dadin magana na fada wa kowa Ina kake ina ka shige dan tawalwali na In zagaya ince wa kawaye ga gwani na In durkusa gaban mai hada duk nazarina In babu kai ashe zai zama naga ajali na Labarina Inzo hira a tashi ban fada ba Labarina Masoyina ka soni hagu da dama Labarina Idan kai ka fade shi ban musa ba In baka rai ashe gaka ka soni ba kadan ba Zare na so na soyayya bai nade wa kowa Da ya nade ni chan zuciya sai na kama kewa Na kamu na riga na kamu bani da ta cewa Kaunarka ke ta kara bugamin cikin jikina Na durkusa na dama fura zo kasha gwanina Na samu wanda yayi anniyar gyra lamari na Ganinsa ne ke karfafa jijiyar ganina In ka tafi ashe zai zama naga ajali na Labarina Inzo hira a tashi ban fada ba Labarina Masoyina ka soni hagu da dama Labarina Idan kai ka fade shi ban musa ba In baka rai ashe gaka ka soni ba kadan ba So gamun jini haka ma suyi ke cewa Shi ko marayi wanibin ya ganshi yawa Ni da na shige sai yamin kamar alawa In na tsosi nan sai in tsosi chan mukewa Ya masoyiya fito na daina kewa In kin bani dama in baki har kushewa Yanzu zuciya ke kadai kawai take kullawa Yaya zanayi gara in soki duk jikina in more rayuwata In more rayuwata In more rayuwata In more rayuwata In more rayuwata Allah yasa mu dace Ameen