Kishore Kumar Hits

Nazir M Ahmad Sarkin Waka - Ja Kulle da Mukulli Bashir Jamoh lyrics

Artist: Nazir M Ahmad Sarkin Waka

album: Labarina


Na kulle da mukuli
Harshe da hakori
Mata ne da ma burgi
Bashir Jamo dai yana nan
Kuce DG yana nan
Chiroman Hausa ganga
A lissafin kida taku gaba ne takun dawakai
Mai tafiya ka kai gaba, shi mai akuya kar ya gusa
Yaro guji kura
Kowa na da mafari
Bashir DG na nimasa
Ni nace gaba tafi
Mata ke da mayafi
Na Na Na Na
Na Na Na Na
Na kulle da mukuli
Harshe da hakori
Mata ne da ma burgi
Bashir Jamo dai yana nan
Kuce DG yana nan
Chiroman Hausa ganga
A lissafin kida taku gaba ne takun dawakai
Mai tafiya ka kai gaba, shi mai akuya kar ya gusa
Yaro guji kura
Kowa na da mafari
(Kowa na da Mafari)
Kai yaro iya allon ka, sarki ke da madoki
Maza duba madubi, Mata ke da yawan sura
Mukuma ke da ma'auni
Kwarya tafi Kwarya, in ta jingina kan dutse ta kwace wa mafari
Na Rantse
Kuji zanchen nan, karya bata da an-nuri
Saura na ta dakon buri
Mu motar da muke turi, in ta tashi tana turi yanzu zata ga dazu
Na Na Na Na
Na Na Na Na
Na kulle da mukuli
Harshe da hakori
Mata ne da ma burgi
Bashir Jamo dai yana nan
Kuce DG yana nan
Chiroman Hausa ganga
A lissafin kida taku gaba ne takun dawakai
Mai tafiya ka kai gaba, shi mai akuya kar ya gusa
Yaro guji kura
Kowa na da mafari
Bashir bai kin mutane
Ya saba da makwabta ne
Bashir mai taimaka ne
Ya buda wa mutane ne
Bashir MD mutane
Ya duba wa iyayye nai
Yana son masu so ne
Ya tattaka mataki
Ya dace da makwarki
Ya inganta makwanchi
Bashir dan maluma, hirar ka ake har saudia
Har nan gaba zai kai ba biya
In ga tawada in ga zuma, shafin gaba to sai mai karatu
Na Na Na Na
Na Na Na Na
Na kulle da mukuli
Harshe da hakori
Mata ne da ma burgi
Bashir Jamo dai yana nan
Kuce DG yana nan
Chiroman Hausa ganga
A lissafin kida taku gaba ne takun dawakai
Mai tafiya ka kai gaba, shi mai akuya kar ya gusa
Yaro guji kura
Kowa na da mafari
Mai dadin zance
Mai Murya kwance
Shi Dan Malam neh
Jikan Malam neh
Mai san Allah neh
Mai san kawa neh
Mai Addini neh
Mai kishin jama'a neh
Yaro gwadi baban ka, baban zashi gwada min kai
Yaro gwadi yayan ka. yayan zashi gwada min kai
Kai nuna abokan ka, abokan sai su gwada min kai
Yayan mu yana Sallah, bai bata wa ma mutane bah
Bai cuta ma makwabta bah
Bashir Jamoh harsashi
Zance neh na mutanen Zaria
Sune suka sa mai Maliya
Bangon talakawan duniya
Na dauki kidi na nai niyya
Baitin da nikeyi mai kaffiya
Zan kai wa makwabta
Na Na Na Na
(Sama lai-lai)
Na kulle da mukuli
Harshe da hakori
Mata ne da ma burgi
Bashir Jamo dai yana nan
Kuce DG yana nan
Chiroman Hausa ganga
A lissafin kida taku gaba ne takun dawakai
Mai tafiya ka kai gaba, shi mai akuya kar ya gusa
Yaro guji kura
Kowa na da mafari
Bashir Jamoh DG Nimasa
DG Jama'a
DG Kasa
AD da rabo, tun farko ka samu yabo
Kasamo ta karbi rabo
Allah MD cikin sanyi an kan ga tabo
Turawa sun che a yaba maka
Ka ga maza kai dan dakka
Kazama turmi sha dakka
Kaga kudi ka daukaka
Kagama tushe barraka
Tafiya MD dukka
Bashir Jamoh kyautar mai dukka
Kai kafito kofar dakka
Al'umma sun che dukka
Gwamnan gobe a bar maka
Allah shi zai haka
Kaga Maza ka firgita
Kaduna da kewayen ku
Kun ji kidin gwamnan gobe
Bashir Jamoh mai takkada
Mai biya allo mai rubutu
Kaduna da kewayen ta
Zai zama zamanin Karatu
A nan dai takadda sai tabi allo sai ta wasa
A nan dai mai karatu sai kaga ya sabke hizif sa
A barmu da masu zanchen dan birni
Ma abun mutanen KD
Kaduna da kewayen ku
Kun ji kidin gwamnan gobe
Bashir Jamoh mai takkada
Mai biya allo mai rubutu
Kaduna da kewayen ta
Zai zama zamanin Karatu
Naziru da ke kida ne yaga mutane masu zane
Allah ne yake mutane, su ko mutane suyi tukunnai
Idan har yaudara nai, bamu cikin tutar mutanen KD
Kaduna da kewayen ku
Kun ji kidin gwamnan gobe
Bashir Jamoh mai takkada
Mai biya allo mai rubutu
Kaduna da kewayen ta
Zai zama zamanin Karatu
Bashir Jamoh mai mutane mai hikima
Ajiyar mutanen KD

Поcмотреть все песни артиста

Other albums by the artist

Similar artists