Kishore Kumar Hits

Ali Jita - Sallama lyrics

Artist: Ali Jita

album: Sallama


Jita ta more duniya, dadi gun kadinta
Wake in koh ya samu jita dadin fadi
Lale-ee-ee-eh lale duniya
Salamu'aikum sallama nake na kara
Kon kon koh ince daku an fara
Ali Jita ne, ku kirani zakin waka
Wace ke bacci in-ta ji ni sai ta farka
Lalai za'a ce damu sam barka
Kwarya za'a bawa me yin shika
Jaki shi yake da jure duka
Kaya harda kai wuya ke dauka
Lalai ba'a cewa babba yaro (aye)
Mai albishir yake da karban goro (aye)
Duk jarumi yana a bayan hero (aye)
Ashe mai akushi yasan da babban daro (aye)
Kumah dan gida yana wuce karoro
Zabe na mai uwa a gindin murhu
Komai na damuwa a nemo sulhu
Ita daukaka kuce nufin Allahu
Haske ku yarda magani ne na duhu
Ga tushiyar kwarai masomin dawa
Abi gaskiya asami karfin kwiwa
Jita naku duniya labari
Arziki da sarauta, duniya aka samu
Duniya aka barta
Mai kudi ya more, shiyake shagalin sa
Lalai rayuwar mu tai tasiri (aye)
Lalai kyan halin mutum ne jari (aye)
Kuka sai kanada babban buri (aye)
Mun more rayuwar mu bama sharri (aye)
Kura damuwarki tari tari (aye)
Wayo yau ya maida na tudu yau a kwari (aye)
Lale lale muyi lale da maraba
Tayani mu du-duba, bazan bar maganar ba
Ni ban iya sharri ba, bazan sha wahala ba
Koh banyi sarauta ba, bazan zama bawa ba
Mu dauko da maraba, mu sauke da maraba
Ban zan dau raini ba duk da ban iya fada ba
Ku taso kuji zance, da Hausa da zaurance
Tinani layya ce, gaskiya fitila ce
Ai karya matsala ce, hassada ciwo ce
Kon kon ina amarsu mai tasiri? (Amarya)
Bude kunnuwa kisha labari (amarya)
Kauna tai halinta kui-ta suriri (amarya)
Ba zage zage ba fada ba mari
Zauna lafiya amarya (zauna lafiya amarya)
Sauka lafiya amarya (sauka lafiya amarya)
Kin zama gimbiya amarya (eye-ee-ee-eh)
Ga zinariya amarya (zinariya amarya)
Ki chaba ado fito amarya (chaba ado fito amarya)
Muyai shagalin biki amarya (muyai shagalin biki amarya)
Murfi dan uwan tukunya
Tirmi dan uwan tabarya (tirmi dan uwan tabarya)
Kaunace tasa shi ziriya (kaunace tasa shi ziriya)
Yau dai kin isso amarya
Kuyai hakurin zama amarya (kuyi hakuri da juna)
Karku gani ku zogi sanya (karku gani ku zogi sanya)
Ya amarya

Поcмотреть все песни артиста

Other albums by the artist

Similar artists