Prince production Ga tamburan masoya Ga baitukan masoya Ku fito rawa masoya Ba yara babu manya Shi so ya tara gayya Kuma so ya watsa gayya Soyayya ruwan zuma ce in ka sha ka ba masoyi Soyayya farar zuma ce waccha a yau ake ta yayi Soyayya farin ciki ce mai yaye bakin ciki ce Indai da so da kauna ayi komai daren dadewa Ita duniyar masoyiya ai filin ta bai matsewa Komai duniya tabawa, soyayya ana dadewa Sakon zuciya da lura an aika yana isarwa Ku tambayi zuciyar masoya Ta sarka da bai katsewa Ga tamburan masoya Mai jita yana bugawa Soyayya ruwan zuma ce In ka sha ka ba masoyi ♪ عسسلم سالم, عليكم, magana ta da sallama ce A ciki salo na waka, kuma in sanya dan kwatance Ni na san hali na kauna soyayya ruwan zuma ce Wasu sun sani da baki wasu a karance ko rubuce Su dai tambura na jita ba kashe kunnuwa sukeyi ba Ga tamburan masoya Mai jita yana bugawa Ga sako wurin masoya Kuyi hakuri wajen rikon ta Kar da ku damu dan magwata dan wasu masu shirya keta A kulla rikon amana, tabaraka jalla ya rubuta Ina mafita gurin masoya? Zaku ji ga Ali jita Soyayya tana da dadi Ba karya nake fadi ba Ga tamburan masoya Mai jita yana bugawa Ruwa, iska gami da sanyi Alkawari bazai gusa ba Wani zai so ka ne da rana Da daddarai bai ki ka mace ba Wani zai so ka dan amana Ko bai baka ko kobo ba Idan Allah yai ma masoya ba kai kuka a duniya ba Bude idon ka dubi nawa Bazan sakaci da addu'a ba Ga tamburan masoya Mai jita yana bugawa Mai san ruwa a gora shi ne zaya rabi tulu Chillan cikin mazaje wannan an kira ta delu Soyayya tana da tsari Bata rarrabai kabilu Na saka Hausa nai' misali Idan magana kawai ta kullu Idan hausa ne azanci ba gaza magana nake ba Ga tamburan masoya Mai jita yana bugawa Ya Allah ka kauda sharri Sharrin aljanni mutane Da yan hasada da kyeta sun gaza zaune ko tsugunnai Toh tunda jalla yayi, yaya zasuyi da rai ne? Kuyi hakuri kawai ku barmu Komai kunga kaddara ne Sunyi kadan su chanja wannan, basa chanja kaddara ba Ga tamburan masoya Mai jita yana bugawa Soyayya ruwan zuma ce In ka sha ka ba masoyi ♪ It's Prince on the beat