Ga sa'ar mata, Sa'adatu Al'kyabar mata Sa'adau Nafara wakar Sa'adatu Ina masoyan Sa'adatu Kinzama dutsin tsakar ruwa, sunanki na kara kolluwa Kyauta kamar ki da ke chan ruwa Kinzama giwa 'a rayuwa Ga ilimi Sa'adatu Ga wayyo Sa'adatu Ga fara'a Sa'adatu Mai baiwa Sa'adatu Allahu ya baki kwargini, taken neh mai farin jini Yar hajiya wacce yar wani, tauraruwa che adon gani Fada su ji ki Sa'adatu Ja ragamar ki Sa'adatu Shallalai Sa'adatu Tantabara che Sa'adatu Sunan ki bazaya boyu ba, hana ki badai 'a yanzu ba Kizo anayin haba, haba Baza mu so baccin ranki bah Ki shagali Sa'adatu Ki ta bikin ki Sa'adatu Chaba ado Sa'adatu Ki shin gide Sa'adatu Sannan ki take da kainuwa, har abada baki cutuwa Sai nasara babu failure Ga arziki gunki shakuwa Yar manya Sa'adatu Yar dangi Sa'adatu Sarauniya Sa'adatu Yar lailai Sa'adatu Sam kin fi karfin hayaniya Sannu da fama da dawainiya Sannu Sa'a, goma ko miya Allah ya karai ki lafiya Mata ku che Sa'adatu Maza ku che Sa'adatu Yara ku che Sa'adatu Manya ku che Sa'adatu Sai laishi jarumar ado Rabo kina yin shi gwargwado Hau karaga ko ki hau gado Zauna ki nishin ki, ki ado Gata da daban Sa'adatu Ga hajiya Sa'adatu Ga mai gwal Sa'adatu Masu dalla Sa'adatu Kin kora karyar mahassada 'A ta Sa'a yar farin gida Zakanya sam ba rabon kuda Akan ki sai maiyi amada Bude ido Sa'adatu Sa sarka Sa'adatu Yi murmushin ki Sa'adatu Sa'ar mata Sa'adatu Allah ya kare shirin wasu Allah ya biya addu'ar wasu Aniyyar magauta ta chin masu A dauki wakar a kai masu Sa'a, Sa'adatu Sa'a sannun Sa'adatu Sa'a sannun Sa'adatu