Sannu sarauniya Rukayya Wanka gunki zasu koya Gimbiya yar dagwas Rukayya, dan Allah gabansu juya Kinzama garkuwa Rukayya Kiyi magana ki tara gayya Mai halin kwarai Rukayya Kece mai dubun masoya Tauraronki na dagawa Mai haske kamar Surayyah Menene gimbiya Rukayya? Wake damun Rukayya? Mai hakuri ina rukayya Yar asali Ina Rukayya Kyakyawa gimbiya Rukayya Wanka sai wajen Rukayya Akwai tsafta wajen Rukayya Ina buga tambaran Rukayya Mata nata tambaya Giwa za a bata girma lallai babu magiya Ai inkaji wance wance ce, domin tai gwagwarmaya A duba Rukayya gimbiya Tun yarinta da tarbiya 'Yar manya 'yar sarakuna, kune ke haska duniya Dubu tasha gaban dari, dagani ai babu tambaya Kura kuma bata cin kashin gwiwa sai dai ta gwagaya Ga dan kolo da malami, sai an raya tsangaya Yara kunga Rukayya jaruma, nidai nabada inkiya Sannu Rukayya sannu-sannu kowa ke yawa maraba Sai nasara da dadadawa, sam bakisan bakin ciki ba Allah neh yake tsareki, ba boka da dan Adam bah Yanzu yabo muke agunki, ba kago halin muke ba Muyi jita musa sarewa, bazai chanzan salan kidan bah Yan yara nata har-harakawa, manya ma ba'a hana ba Mun tina toshiya ta dauri, bazance kara bace ba Linzamin ya girma kaza, koh akuya bata nada bah Sama dai ta darar ma yara, sai hange basa taba ba Yanzu Rukayya ce a fili, tauraronta bai dishe ba Kainuwa dashin Allah, yanzu Rukayya tafi karfin su Mai gado na zinari kece zaki gaji Balkisu Kiyi ado na alkeba mata na kiranki dawisu Wacce duk ta zageki lallai zata dinga nida su Rukayya ai sarauta ce mata sun fada da bakinsu Masu so suje bude ido nan zasu kara kallonsu Masu so abasu abasu nan zasu mika hannun su Sannu dai Rukayya, Rukayyatu gimbiya ta mata Sannu dai Rukayya, Rukayya jaruma ta matan duniya