Kishore Kumar Hits

Umar M. Shareef - Kyakkyawar Fuska lyrics

Artist: Umar M. Shareef

album: Farin Jini


Kyakwawar fuska na kalla ta deben kewa
Kuyi min san barka na samo fitilar 'yan mata
Kyakwawar fuska na kalla ta deben kewa
Kuyi min san barka na samo dan auta na maza

Masoyiya, masoyi na kai ne
Aminiya, aboki na kai ne
Ke zuciya, rabin raina kai ne
Ke jijiya, jinin jikina
Kin zama komai na, abun kallo madubi na
Kai ne tinanina a barci na da mafarki na
Ban bari ki cutu
Zan zama garkuwa
Komai yake zuwa
Gareki zana tare shi

Adadi na ruwan sama wanda suke zuba
Adadin kifaye ma ba a san su ba
Adadin bishiyoyi baza su kirgu ba
Haka soyayyarki a rai ban santa ba
Koda za'a au'na ba sikele wanda zai dauka
Bata misaltuwa soyayya wace nake miki a zuciyata
An san farkon rikici, ba a san karshen sa ba
Soyayya gamu ciki, baku san haduwar mu ba
Alkhairi ne a ciki, sam sam ba sharri ba
Karda ku ce, "Zaku raba, bazaka ku iya ba"

Zan fesa turare
Inzo in zauna in bude hakore
In ta murna, Allah sarki zare
Dukanin fargaba
Angoye amare
Mu a nuna ni dake a tare
Zamu zauna rayuwa ta kare
A tare har abada
Kawaye ku kalla
Shi na ba akalla
Wanda bai so nai kwalla
Nima bana so yayi
Ke na tsayar zabi na
Na sanar dangina
Zana turo abba sa rana ayi
Wajibi in kwantar da kai
Munyi aure ni da kai
Karshen biyayata ga kai
Zanyi tunda ina ji da kai
Kyakwawar fuska na kalla ta deben kewa
Kuyi min san barka na samu fitilar 'yan mata

Поcмотреть все песни артиста

Other albums by the artist

Similar artists