Na fada na kara Nima na riga na furta Na riga na tsara Na riga na shirya Na fada na kara daga ke ba kari Na fada na kara daga kai ba chanji Yadda dai kinka kin na gode Sirrikanki gare ni kin bude Nagani duka na rude Nima nawa gareki zan fede Yarda takai yarda Ni dake babu boyen sirri Abun nema ya samu Zuciya ba abunda yake damu Yiriyiri kawai ya rage mu Dauren aure allahu ya kai mu Daga zarar kowa ya shaida Soyayya ba sauran buri In kai baiwa allahu zabi shikenan Ka huta ba ka ba wahala kenan Kai ta adu'a sai kadan yi jira sanan Hakuri matakin na cin nasara kenan Tabbas komai lokaci ne Allah sa muga alkairi Yaushe ne yaushe ne auren mu masoyina? Yaushe ne za'a sa ranar mu masoyina? Yaushe zamuje ga gano dangi da iyaye na? Yaushe zaka kawo kudi gidan mu sadaki na? Wallahi nidai na kosa A cikin kawaye in wuce gori Bazan yi aure idan ba dake ba Bazana goyi 'dan da ba naka ne ba Duk wace ta kirani ma bazana zo ba Komai ake nuna min bazan gani ba Kauna ta kai kauna Kaine karshe kaine fari