Kishore Kumar Hits

Umar M. Shareef - Wayyo Ni lyrics

Artist: Umar M. Shareef

album: Farin Jini


Wayyo ni wayyo ni rayuwa
Tasa na shiga damuwa
Ga sanyi ga kishin ruwa
Sabon labari
Farfesu yaki dafuwa
Kasa wuta sama ga ruwa
Daga ji kasan da damuwa
Ba mai yin kari
'Da ya zauna cikin uwa
Amfanin rai rayuwa
Mai tarbiya yafi moruwa
Dan baya sharri
Motsin kifi cikin ruwa
Zancen na inda karuwa
Zo ku fahimce ni 'yan uwa
Bani nufin sharri
Share hawayenki yar uwa
Dama sai yayi faruwa
Kaddara ce a rayuwa
Wata ran sai labari
Kuso maso kaunar ku 'yan uwa
Karda ku sanya su damuwa
Muhimmanci nasu da yawwa
Tari tari
Budurwa ta zama tsohuwa
Tilas ne inda rayuwa
Ba mai hana shi faruwa
Allah yayai tsari
Ba cuta babu cutuwa
Da tsuntsu an samu tsuntsuwa
Halitun Allah akwai yawa
Tari tari
Kakani sunyi ganuwa
Dan ya zamo musu garkuwa
Daga sharrin wanda ke zuwa
Tsohon labari
Karda ka zam mai shagaltuwa
Kun nema kaita damuwa
Ibada baka san zuwa
Hakan ba alkairi
Numfashi na ta raguwa
Mutuwa ce dai take zuwa
Maza shirya kunji 'yan uwa
Da aikin alkairi

Wake shuka saman ruwa
Allah gatan mu rabuwa
Barta da zanenta zabuwa
Shine alkairi
Wanda ya yima kafafuwa
Kune hanci idanuwa
Numfashi kai ta rayuwa
Kuma ba yayai ma gori
Shi ya halice mu 'yan uwa
Muyi laifi yayi afuwa
Muyi roko yayi karbuwa
Yayai kyauta yayai kari
Alkairai nata yaduwa
Kullum suna kara daduwa
Alfarma ce muke hawa
Ta hasken annuri
Baban Fatima garkuwa
Annabi sa muyi abin hawa
Kai na rike bani faduwa
Toshen alkairi
Allah sa rana ta mutuwa
Ta zamo min tafi soyuwa
A guna na mori rayuwa
Ba sauran buri

Поcмотреть все песни артиста

Other albums by the artist

Similar artists