Oooh haaaaa Aaaaa haaaaa Yardaaa ce tasa ake jin sirri na Juna nawa gunki Zan fada Ki rike amana Yardaaa ce tasa ake jin sirri na Juna nawa gunka Zan fada Ka rike amana Haske tunda kin fito shi nake gani Gefenki nan na karkato ba'a ja dani Domin a sonki na fito, karki tadani Na hau jirginki na fito Ki hayar dani Kema Haka Nai zato Sam bayani Cemin jarumi huto kwanta araina Taka ce ni ku shaida kawaye Babu shauni Muje gun Iyaye Ina da rauni amma zan kiyaye Matsayi Ka bani mai sharen hawaye A cikin rai da zuciya kayo kawanye Kauna ce ta zagaye a jini ta Zauna Matsonan masoyiya kisha labari Na so Wanda zaya sa kiyo annuri Da kyautar da zaki bani shinee Tsari Kafin na fadan abinda Ke ranki a buri Inna ji zanyi hanzarin nawa da wuri Zan furta a sarrari sirri na raina Tatsuniyar gizo, Koki kwarai Dodo daya muke Wa tsafi sarai Burina shine naka aure idan da Rai In karya nai fada anaji garai garai Taso zo Muje mu Zauna a cikin furai Muyi kallon kyawawan tsirai Dadi na raina Shi So tsuntsu yake (Tsuntsu yake) Na sanyo fiffike kanki na duro Gayu na tsallake (kin tsallake) Gasu a daki cike, Kai na ciro Hanya daya dani dake mun Kai Karo So a zuciya tsaro Mun Kama juna Yarda ce tasa ake jin sirri na juna nawa gunki Zan fada Ki rike amana Yarda ce tasa ake jin sirri na juna nawa gunka Zan fada Ka rike amana