Kishore Kumar Hits

Umar M. Shareef - Ni Da Ke lyrics

Artist: Umar M. Shareef

album: Ni Da Ke


Da ni da ke
Da ni da ke
Da ni da ke
Soyayya
Da ni da ke mutuwa zata raba mu
A zuciyata ke nasa banyi ko zato ba
Rabin jikina, bazan rayu babu ke ba
Babu sukuni in ban gano ki kusa dani ba
Waye zai fada ni da ke bamu yo dace ba
Nasan kinyo tako dani
Ko ina dole a san dani
Manyan yara su gaida ni
Da ni da ke mutuwa zata raba mu
Alkawari nayi da ni da ke mutuwa zata raba mu
Da ni da ke
Da ni da ke
Da ni da ke mutuwa zata raba mu
Kin kula dani a soyayya ban manta ba
Kinsha gwagwarmaya da magauta ba dan kadan ba
Kushe da zagi bai san ya ki canza ni ba
Idan da halacci bai kamata na yada ke ba
Masu kudi da dama wadanda sun fi ni ba kadan ba
Sun baki kudi da mota kallon su bakiyi ba
Kince dole sai ni kuma nima bazan guje ba
Komai ruwa da rana (nasan ba zata barka ba)
Komai zafi da sanyi (Umar ba zata barka ba)
Koda za'ayi ta duka na
Nasan da masu zagi na
Babu tsoro cikin raina
Da ni da ke mutuwa zata raba mu
Alkawari nayi da ni da ke mutuwa zata raba mu
Na ni da ke
Da ni da ke
Da ni da ke mutuwa zata raba mu

Yau na gane so-so-so
Eh yau na gane so (soyayya ba kudi bane)
Sannan na gane (soyayya ba mota bace)
Mr. Bangis yace mini (soyayya ba kyawo bane)
Shine yace mini (soyayya ba mulki bane)
Kuma kowa ya gane (soyayya ba sarauta bane)
Ya sake fada mini (soyayya ba sutura bace)
Wallahi nidai na gane (soyayya ba'a harshe bane)
In kudi ne (ni nasan ba zata so ka ba)
In mota ne (ni nasan ba zata so ka ba)
Idan mulki ne (eh nasan ba zata so ka ba)
Kai idan kyawo ne (sam nasan ba zata so ka ba)
Ba zan barki ba
Ba zana barki ba
Ba zan barki ba
Ba zana barki ba
Da ni da ke (baby, um baby)
Da ni da ke mutuwa zata raba mu

Поcмотреть все песни артиста

Other albums by the artist

Similar artists