Kishore Kumar Hits

Umar M. Shareef - Bude Cikin Zuciya lyrics

Artist: Umar M. Shareef

album: Ni Da Ke


Bude cikin zuciya ki jefa ni
In na shige sam kar ki fidda ni
Bude cikin zuciya ka jefa ni
In na shige sam kar ka fidda ni

Dan mazari a kira gwanin rawa, in ya fito tilas a yo kalla
'Yar makaranta na fi so kunga, bani shiri da diyar dake talla
Fidda gwanin ki kice ba gani ba, je a gari kiyo shela
Nine na zama zabin ki
Daurin auren mu nayi doki
Taron auren mu za'ayi taron bikin da ba a taba yi na dangin mu

Na guji samarin zamani sun sanya budurwa tayi kwalla
Mai kwadayin sabon zani itace gayu ke yiwa illa
Nayi addu'an samun miji nagari kullum in nayi sallah
Dakai ya hadani a duniya
Rayuwar mu muyi ta musha miya
Nayi fata ko a lahira mu zamo tare a cikin aljannar mu

Taro da kwabo in har na samu ke zan ba ajiya
Domin yin amfani gare mu kai har ma da iya
Albarka sa tasa ki dube mu yau mun zarce jiya
In mun bisu cikin lamarin mu muyo nasara
Hannu kyauta shike samu in har ya tara
Mudai sai dai fa mu kara godewa ba abinda yake damun mu

Rikita-rikita ne alkawari ba zan sanya ka kuka ba
Kwarin gwiwa na karama bazan sa kayo rauni ba
In mun samu mu gode rashi ba zai sa muji komai ba
Allah shine ya bamu
In yaso baya bamu
Sai yanda kaso kake yi alkhairi ka sada mu

Bude cikin zuciya ki jefa ni
In na shige sam kar ki fidda ni
Bude cikin zuciya ka jefa ni
In na shige sam kar ka fidda ni

Поcмотреть все песни артиста

Other albums by the artist

Similar artists