Idan ki ka ce ni ne, ba zan ba ki kunya ba Ni ma za na ce ke ce, zabi na Tun da har ka ce ni ce, ba zan ba ka kunya ba Ni maza na ce kai ne, zabi na ♪ Kece wacce na ke yin nuni, sinadari na Tarrayya da ke zan tare, mahadi na Ungo na sa ko mi ki tsani shigo gidana Ba bu mai mini kallon raini uwargidana Na san in na aure ki Ba zan kwana da yunwa ba Tun da kin kware gun girki, iyalina ♪ Soyayya muke don Allah, iya sani na Shi ya sa mu ke da da danko tare da juna Alkhairi muke so mu kulla da masoyina Ko da yaushe in nai sallah a addu'a na Allah sa na zam taka Mai kula da hakinka Farin ciki zan tara maka A dakina ♪ Mun yi gaba mun huce Mun yi nisa mun bace Kamar hannun Agogo Ba na jin bugun ice Na yarda in mace Na kai ga Bango A mike ba bu karka ce Ba rabewa kai ka ce Waka na ke da dango Zan yi yarda kai ka ce Ni masoyiyar ka ce Jarmi dabam da rabgo Soyayyar ki ba raini Ba zan yi asara ba Kun biyan kudin dinki Iyalina Idan ki ka ce ni ne, ba zan ba ki kunya ba Ni ma za na ce ke ce, zabi na Tun da har ka ce ni ce, ba zan ba ka kunya ba Ni maza na ce kai ne, zabi na