Kishore Kumar Hits

Umar M. Shareef - Koko lyrics

Artist: Umar M. Shareef

album: Ni Da Ke


Koko
Koko
Mai ganga doko haya

Bismillah Allah na kirawo da farko
Duk abinda nake yi shiyake bani iko
Shike kareni in andana mini tarko
In yaso insamu na shayi ko na koko
In na rero wakata ganga na doko
Guna yan mata da samari shako
Suyi rawa da kidana a sannu in tura sako
Duniya labari kunji shafi da farko
Wani ya saki mata wani an mishi baiko
Wasu sun subda wasu dauka su wanko
Wani ya kare wani zai fara da farko
Duniya nagane tana ajewa ta dauko
Musulunci shi yace mu karama bako
Mata a gida koh su zauna kar su leko
In kana nema Allah kadai zaka roko
In yabaka ka gode mai kuma sai ya ninko
Gaskiya ka riketa a ko ina kayi karko
Dauki wanda kakeso in baiba ka sako
Hausawa muke zauna yarabawa dunko
Dankali a hako kwaiba ita sai tsinko
Zabi wace kake je ka ai muku baiko
Kwanciyar mai sanyi zafi koh ya narko
Zana zabi tuwo da miya in za'a girko
Shukar da mukayi wata rana za'a hako
Rabbi samu mu dace lahirar mu ta hasko
Kuskuren da mukayi yafe mana kar mu dauko
Domin darajar manzon nan daka aiko
Na kira shi da konko
Mai rayuwar dan tsako
Ya hallata ayi ko
Matarka jeka dauko
Kasakata a boko
Islamiyya shine farko
Sunnah ta ma'aiki muyai riko
Tashi tashi kuzo muyi sanmako
Bani raina sana'ar mai dako
Addu'a ta zarce ruwan jiko
Allah ka tsare mu ga mai fako
Tafiyar kai yafi kayo rako
Godiya Allah mai iko
Shi yayai mini kafar dana tako
Da hanuwa ganga na doko
Shi nake yin roko
Shi nake yin roko
Shi nake yin roko

Поcмотреть все песни артиста

Other albums by the artist

Similar artists