Kishore Kumar Hits

Umar M. Shareef - Nazari lyrics

Artist: Umar M. Shareef

album: Ni Da Ke


Nazari mudinga nazari
Nazari mudinga nazari

Kafin farawa gareku sai nayi sallama
Abokai da yan uwa ga hanuna ku kama
Nine naku M Sheriff dan karamin alarama
Jariri a cikinsu mawaka ne wata rana a sama
Ni nazo da yar nasiha ta gun al'umma
Idan an maka shari dan uwa karda ka rama
Wanda yasha madaci yau gobe kaganshi da zuma
Mai gona ta shari shine zai girbi nadama-aa-aa-ah

Nazari
Mu dinga nazari
Nazari nazari
Nazari
In kaji anayin zancenka kai ka kai ayo ne
In kadau wachan masoyi wani makiyi ne
Ka wuce anata zagi wasu kuma yabo ne
Ni dan nagane sai na toshe kunne
Kaima ka toshe kunne bar hangen wane-wane
Abinda Allah yaso kasamu wajibi ne
Komai a hankali ne rayuwarmu tana a zane
Rabon ka bai wuce ka koda kana a zaune
Kukan kurciya jawabi ne inji mutane
Ni koh inda zanyi nawa a baituka ne
Karka fida rai da samu in kana araye
Karka fida rai da samu in kana araye

Nazari
Mu dinga nazari
Nazari nazari
Nazari
Duniya duniya ce makaranta harda malami
Dauki takandaka ka karanta da alkalami
Karda ka yarda ayi maka rata dinga azumi
Karka biyewa zuciya ta saka ka zauce
Nemi tsari ga rabbi shedan kanka kar ya dace
Addu'a ga mumini tazama garkuwa ce
Allah sa mudace
Zunubai mu kauce
Toh sai mu jajirce ayyuka mu nace
Nafi so ingani a sahun farko
Nai yin murna da samun sakamako
Kyakkyawa da an kira ni in miko
Dacewa gun ihahu mui nema ba dan adam bah

Nazari
Mu dinga nazari
Nazari nazari
Nazari

Mu dinga nazari

Поcмотреть все песни артиста

Other albums by the artist

Similar artists