Zo kusantu dani Zana rayu dake Amana ta kaina zana baki Zo kusantu dani Zana rayu da kai Amana ta kaina zana baka ♪ Na aminta dake, mu zauna rayuwa tare In za kiyo zance, ni kuma zanyi saurare In baki tukwuici, zaba da kanki balango ko tsire? Ki diba ki more, kauna ce tasa komai zanyi miki Zo kusantu dani, zana rayu da kai Amana ta kaina zana baka Idanuwa ke suka buri, a koda yaushe su gani Fuskar ki na dauke da nuri, kalle ni in zamma gwani Cutar so dake yin ruri, ke kika zamto magani Yanzu kowa ya ganni, banda damuwa sai tsantsar farin ciki ♪ Abin kamar wasa, a son ka gani nayo nisa Kuzo muyo gasa, yanmata sai kun sha kasa Ni nuna zabin sa, haka nima shi kadai ne ya isa Sadaukar da raina, a gare ka wannan karamin aiki ne Zo kusantu dani, zana rayu dake Amana ta kaina zana baki Farin ciki na karuwa, idan na ganka a dama So zai zama samu a rayuwa, tunda a kullum ina nema Nayi godiya da dadawa, gun wanda shi ke ban dama Bana yin nadama, haduwar mu ta hana inyo bakin ciki Zo kusantu dani, zana rayu dake Amana takaina zana baki Zo kusantu dani, zana rayu dakai Amana ta kaina zana baka