Azima ke nake wa so na hakika In ba ke ba babu wacce zan ba kauna ta Ni Azima kai nake wa so na hakika In ba kai ba babu wanda zan ba kauna ta ♪ Zuciyata ke take muradi Ke kike sawa inyo nishadi Dan matso nan kusa muyi tadi Babu wai-wai a so ana jihadi Kisa atamfa zani saka yadi Muyi fes-fes mu zagaya a gan mu a nuna Kai na hango na taho gare ka Da furen so shi nazo in baka Tunda kasan bani da kamar ka Jinjina ta nayi a gaban ka Nayi biyayya ban bari ka koka Tunda Aljannah ta tana kafar ka mijina Azima ke nake wa so na hakika In ba ke ba babu wacce zan ba kauna ta Ni Azima kai nake wa so na hakika In ba kai ba babu wanda zan ba kauna ta Zo Azima masoyin ki na kira Ki bani dama to ba nayi miki hantara Na samu girma sanyi a rai na kankara Tunda ni kike so haka nima sai ke Ba nadama gamo dakai ka ankara Zan yi tsama da makiyin ka ba jira Karku soma ku ja da baya hattara Tunda ni kake so haka nima sai kai Azima ke nake wa so na hakika In ba ke ba babu wacce zan ba kauna ta Ni Azima kai nake wa so na hakika An sani dani dake mun saba da juna Bani yin sake kin zama 'yar lele na Zan yi rayuwa dake har karshen rai na Su gani da kansu kece zan nuna Kyawun shigar ki ta zarce a raina Ki fito su gan ki dawisu a guna iyyeh Duk abinda zaka yi mini masoyi na Baya sawa inji haushin ka cikin raina Tunda na riga da na narku cikin kauna Ni da kai kadai nake so in gana In kaje dani hakika zan shana Babu wanda zaya kalle ni ya raina iyyeh Azima ke nake wa so na hakika In ba ke ba babu wacce zan ba kauna ta Ni Azima kai nake wa so na hakika In ba kai ba babu wanda zan ba kauna ta