Kin hadu 'yan mata Kinji manufa ta Soyayya na zo ki bani Ki mai dani dan gata Kin hadu yan mata Kinji manufa ta Soyayya na zo ki bani Ki mai dani dan gata ♪ Bani yin karya Lokaci daya Son ki yayi mini mamaya Kira ni na shirya Gani kan hanya Gun ki zan zo da soyayya Sako na zuciya Ba nayi buya Zani nuna ma duniya Na sako kaya Na ci kwalliya Na taho ne mu gauraya Ke nake kallo Hasken ki ya bullo Ya saka nai ta zillo Ke zaki mini gata Kin hadu yan mata Kinji manufa ta Soyayya na zo ki bani Ki mai dani dan gata Kin hadu yan mata Kinji manufa ta Soyayya na zo ki bani Ki mai dani dan gata ♪ Da na nufo gun ki kin kauce Zuciya tawa kin sace Inda zaki so ni kin dace Ruwan zuma ungo zaki ce Kina cikin raina Safiya dare rana Ko na mace babu raina Da son ki zana kwanta ♪ Dan matsa baya Kaji dan karya Na wuce ma a tarayya Ba kajin kunya Ka taho gaya Ni kake cewa soyayya Ka fara ma buya Ko a kan hanya Bani so daina bibiya Na shige kurya Kai kana baya Karka sa nayi ashariya Kwarya tabi kwarya Gaye cire karya Dai-dai da kai je ku shirya Ni nayi ma rata ♪ Oh kin hadu Ni nace kin hadu Kin hadu, kin hadu, kin hadu 'yan mata Kin hadu 'yan mata Nidai kinji manufa ta Soyayya na zo ki bani Ki mai dani dan gata ♪ Kin hadu 'yan mata Kin ji manufa ta Soyayya na zo ki bani Ki mai dani dan gata