Haduwar mu tasa farin ciki a raina Yanzu ke kadai nake ra'ayi Haduwar mu tasa farin ciki a raina Yanzu kai kadai nake ra'ayi ♪ Na tsaya dake a so jaruma Ke nake shirin yi wa hidima Kyan ki kesa jiki yake tsuma Ke na zaba abokiyar zama Hankali yana kan ki na gano alama Shi kadai ya isa nayi fahari ♪ A tambaye ni wa na tsayar gwani Amsar sa kaine ba yau ba tuntuni Ni taka ce na baka izni Saka ni ran ka ko'ina kaje dani Zan taho ba jinkiri sanda ka kira ni Tunda dai kana da kyan nazari Haduwar mu tasa farin ciki a raina Yanzu ke kadai nake ra'ayi ♪ Haduwar mu tasa farin ciki a raina Yanzu kai kadai nake ra'ayi Ayo rubutu, sai mai karatu Cikin batu, in nayi kure ki gyara Lallai na fahimtu, kuma na iliman tu Dadin batu ya sani bude hakora Ilimi ake dashi bai barin babatu Ni da ke mu dinga yin hakuri ♪ Ina bayani, muna kamanni Da kai da ni mun zamo daya Na warke rauni, kin karrama ni A sansani ke zan gano ke daya Dan Adam a rayuwa na da rauni Don haka mu dinga yin uzuri Haduwar mu tasa farin ciki a raina Yanzu ke kadai nake ra'ayi Haduwar mu tasa farin ciki a raina Yanzu kai kadai nake ra'ayi