Yaki a soyayyah na shirya taho mu buga yan mata 'Yan mata, ah-ah yan mata Yaki a soyayyah na shirya taho mu buga dan gata Dan gayu, ah-ah dan gata ♪ In kinka dau kibiya, ni kuma zana dau mashi Ba zana motsa ba, indai zaki harbo shi Zan sanya kirji na, ba tsoro in tarbe shi Cikin zuciyata, ai nan ne masaukin shi Kinyo nasara a cikin yakin ki dauki shi Kin zamto sarauniya duk mata kece da kinga gaba manufata Manufata ah-ah Gani na isko ka gaba da gudu, in na isko ka sai nishi Indai da soyayyah, tabbas akwai kishi Kai dai zana ba rance tunda kana biyan bashi Ka harbe ni, zana tsaya da harsashi Na soyayyah, baya kisa koya tashi Tun ranar da ka same ni dashi jina nake kamar wata autar mata Autar mata Sun koma da sun ganki, kin masu kwarjini Sunyi bugu sun barki, kin sasu hawan jini Soyayyah ta taki, zo ki kula dani Indai na aure ki, baki guna-guni Naji giyar soyayyah, kin shayar dani Nima dole in baki nawa don kiyi masu rata Kiyi masu rata ♪ Haduwa ta dakai tayi riba Lokaci guda munka saba Ka zamo madubi na duba Abinda kaso inyi, zanyi shi ba aibu ba Aure na sanya a rai, dakai ka zamto uba Mu hado zuri'a dakai shine manufa ta Manufata Cikin su mazaze, ai kaine auta na maza Cikin mataye, ai kece autar mata Ra'ayi kuma riga, je ki dau dankali ni gwaza A raina na sanyo ki, na baki kula yar gata 'Yar gata 'Yar gata, ah-ah yar gata Dan gata ah-ah dan gata Yaki a soyayyah na shirya taho mu buga yan mata 'Yan mata, ah-ah yan mata Yaki a soyayyah na shirya taho mu buga dan gata Dan gayu, ah-ah dan gata