Nayi hasashe Hasashe Hasashe na ya tabbata gamu a tare cikin soyayya In bake sai na jikita yaki taho zo muyi tarayya Hasashe na ya tabbata gamu a tare cikin soyayya In bakai sai na jikita yaki taho zo muyi tarayya ♪ Tafiya komai sannu-sannu ake farawa Dokin hakuri duk wanda ya hau shi yana dacewa A tsakani in dai an zauna akan sabawa In an sasanta dai-dai ne shine morewa Kaina na baki, na zam naki Kallan da idanun ki Ya sakan shauki ♪ Kai zan ba zobe, ka saka shi a hannun ka Bana so mu rabe, ka saka ni a kirjin ka Kai na kira gwadabe, ka bani takobin ka In ka ban zani cafe, ammah sai na duka Biyayya zan nuna, kullum in gaishe ka Na barsu mahaifa na, na yarje zan bika Hasashe na ya tabbata gamu a tare cikin soyayya In bakai sai na jikita yaki taho zo muyi tarayya Ta daban ce ke ta daban, a ciki ke na ware Ku raba mu kunyi kadan, in kunka matsa sai kun zare Mutuwa ne zanyi idan babu ke sai na haure Lafiya ta kece indai baki kwarai bani Na tsaya na nace bani gudu sai an bani Abari ya huce shike bada rabo ga wani Hasashe na ya tabbata gamu a tare cikin soyayya In bakai sai na jikita yaki taho zo muyi tarayya ♪ Hasashe na ya tabbata gamu a tare cikin soyayya In bake sai na jikita yaki taho zo muyi tarayya Ni taka tun asali ba mai kwace ma Ji karka so furari shi nayi rokawa Zani sako kwalli inzo in nuna ma Kai ka saka ni kiba jikina ba rama Hankalina ya kwanta Damuwa tuni na manta da zuwan ka cikin raina (haaa haa) ♪ Idan gaki ba wata mace da zan kalla Diya babba yar makaranta baki yin talla Tafiya ta mai nisa a gidan ki zan bulla Kin kore min komai zai sa nayo kwalla Hasashe na Tunani na Ta nuna manuni gaki nan ga ni Hasashe na ya tabbata gamu a tare cikin soyayya In bakai sai na jikita yaki taho zo muyi tarayya