Na baki soyayya ta Da baki na furta ta Wadan su na neman ta Gare ni ba damar ta Kina ta yin kyama ta Shin menene illa ta Ki so ni zaki huta Ki yo daban cikin mata Komai kike bukata Akwai kudi da mota Diba ki dinga yin kyauta Zan baki dukkanin gata Ke na bida Kin ce, "Ban miki ba" Sai ki fada Mecece matsala ta a soyayya Ke na bida Kin ce, "Ban miki ba" Sai ki fada Mecece matsala ta a soyayya ♪ Soyayya ta gaske da gaskiya Ba karya kudi basa iya siya Tarbiyya ta hana jayayya Sun raba hanya, arziki da tsiya Ni ban ki kaba Kuma bazan so ka Muyi mararraba Da juna sam bamu dace ba Ba kayi mini ba Kuma ba zaka yi mani ba Barni inyi gaba Ina da wanda nake so da soyayya Ba kayi mini ba Kuma ba zaka yi mani ba Barni inyi gaba Ina da wanda nake so da soyayya ♪ Dan gayu nake Ko a cikin su daban nake Yan mata kar kiyi sake Da karfi ni zaki rike Ki yarda mu zauna dake Matata ni ince dake In munyi aure dake Zan baki kula har ace baya ke Nidai ke na bida Kin ce, "Ban miki ba" Sai ki fada Mecece matsala ta a soyayya Ke na bida Kin ce, "Ban miki ba" Sai ki fada Mecece matsala ta a soyayya In dai kayi tunani So bai duban kamanni Kyawu koko muni Ra'ayin haka da akwai ni Inda zaka kyale ni Inje inyi rayuwata ni Da wanda nake kauna ni Kayi min haka ka taimake ni Ba kayi mini ba Kuma ba zaka yi mani ba Barni inyi gaba Ina da wanda nake so da soyayya Ke na bida Kin ce, "Ban miki ba" Sai ki fada Mecece matsala ta a soyayya