Nayi tsintuwar soyayya Budurwa kyakkyawa Gani dai kamar na shirya Ina ta kakkarwa Inje gare ta ne ko na tsaya Na kasa yankewa Kin yi kwarjini a ido na Kina yi mini yana ♪ Da zai yiwu in san sunan ki Na dinga furtawa Ya zamo abin fadi na a baki Nayi ta nanatawa Gani nan ina ta bin sahun ki Ko zanyi ganewa Gidan ku haka zai zam mini sauki Na dinga lekowa Koda ganin ki in nayi da idanu Rai zai farantawa Na kamu da cuta gata a raina ba ranar warkewa ♪ Nayi nisa, nayi nisa, nayi nisa Ba zana dawo ba In na furta kika ce bakya sona Ba zanki kuka ba In ko kika ce dani masoyina Dadi bazan yi barci ba Farin cikin da zanyi a ranar ba zan misalta ba Koba kida rawa zan taka miki Bazan ji kunya ba ♪ Idanuna suka kaini, kafafu suka bini zuciya tana dauki Nasan zan kece raini, zai zamto ba kamar ni, kin kira ni angon ki Kowa nawa aka ce gare ni, indai har za'a bani, zan biya sadakin ki Da zan zamo miji gun ki Zan kare dika hakkin ki Na zam adali a mulkin ki Mai martaba a fadar ki In kira ki suna sarauniya In kira ki suna sarauniya In kira ki suna sarauniya