Zo mu zauna da dake masoyiya Na amince da ke har zuciya Aure ni dake na shirya Amana zan rike ba gajiya Tunda kin mini so da gaskiya Don haka ban barin ki sha wuya Zana kula dake zinariya Na ji dadi wa zai mini barka Nayi godiya a gare ka Tunda ka kira ni matar ka Zana baka duka hakin ka Ni, ni ban yarda ba a kushe ka Na yaba da halin ka Saboda iya takun ka Natsuwar ka, jarin ka, ni na so ka Zo mu zauna dake masoyiya Na amince da ke muyi auren sunnah Zo mu zauna da kai muyi rayuwa Na amince da kai muyi auren sunnah ♪ Ni dake zan daura aure Na zamo ango ke amare Daki na a gida na zaki tare Ki rangwada kwaliyar ki sa turare Farin cikin ki zaya dore Hawayan ki nine zan share Da ke zan zauna na more A tare ba ware Zana jure Mu kore ba ware Allah hore Kai ne zabi Allah yayi mini Naji dadi nima kayi mini Ga hannu na kama ka hayar dani Gidan aure ka kaini ka, kaini A mata zai zama babu kamar ni Domin nasan sai na kece raini Matsayi mai girma kai zaka kai ni Zo mu zauna da ke masoyiya Na amince da ke muyi auren sunnah Zo mu zauna da kai muyi rayuwa Na amince da kai muyi auren sunnah