Kauna ba zato ba tsammani ta shige cikin raina Kai nake wa tayin so amshi kace kana so na ♪ Babu zato ba tsammani furucin ki kamar cikin barci Ni da ke ba zancen so sharadin ki bai kau ba ♪ Asalin soyayyah kai na saka cikin zuci Ina fara tunani naka sai na kasa yin bacci In ka ambaci ya mace sai inji ni ina cikin kunci Zo ka bani ruwa na zuma karka bani mai daci Kai nayi wa tanadin soyayyah Karka barni inyo jinya Riga ta sonka ne na sanya dubi jiki na tayi mini dai-dai ♪ Kece kika ce mini kalmar so kar na furta yanmata Inko na kuskura nayo haka zaki tsane ni mun bata Niko da bani son haka nayi na'am na kira ki kanwa ta Nayi nisa a son wata ni a gani na zamu dai-dai ta Son ta nayo bata Hankali na ya karkata In bata zan haukata dani da ita hadin mu yayi dai-dai ♪ Yau na bayyana ban boye ba cibi ina wanka Zancen dake cikina na fiddo fili ya sha iska Ka mamaye ni ka shiga raina babu shiri ina binka Karda kace dani baka so na zai saka ni nayi kuka Amshi makulli na ka tuka Ko'ina kace dani taka Kowa ya kira ni matar ka Zan amsa sunan hakan nidai ♪ Wacce nake so da soyayyah Na sani tana a kan hanya Zana nuna miki da gayya Aure na da ita na shirya Dube ta nan haka kiyi dubawa, madubi duba Da ita dani mun saba, ba zamu rabe ba Handa ta jini a soyayyah, ba za'a raba ba Fuskar dake ciki ne zabi na rike ni muje dai-dai ♪ Na rude jindadi ka bani kauna Nagode, nagode ka ceci raina Kawo hannun ki nasa zobe na alkawarina Tun haduwar mu a farko so tarkon ki ya kama kauna Nayi haka, nayi haka, na nuna bazan boye ba Nima nayi haka, nayi haka na nuna ka ba jin kunya ba