Kishore Kumar Hits

Umar M. Shareef - Bayan Mutuwa lyrics

Artist: Umar M. Shareef

album: Masoya


Bayan mutuwa bakomai daga kai sai halayyar ka
Bayan mutuwa bakomai daga kai sai halayyar ka
Da sunan Allah na daya
Sarki mahaliccin duniya
Kaine mai mulkin gaskiya
Wanda sam baka yin murdiya
Kai ka tsara mana duk rayuwa
Muyo kuka ko muyi dariya
Rokon da nake sarki daya
Daura ni a hanyar gaskiya
In bar aikata sabo, yazam bana yin zunubi ko daya
Komai in kaso ni zan zamo, sam ba wani mai yin kariya
Bukatu na duka na tattaro, nasan kaine zakayi biya
Nazo neman tuba, laifukan sabo wanda nayo jiya
Wanda nayo jiya, laifukan sabo da nayo jiya
Ni abinda ya sani a damuwa idan na tuna ranar mutuwa
Ranar da bawa zaya zam mai kishi yana neman ruwa
Iyaye, ya'ya, ko yan'uwa, ba wani mai yi maka garkuwa
Dukiya ko mulki ka rike, suna kallon mai ke faruwa
Yansanda ko sojoji, sun zama hoto sannan kuwa
Yanda Allahu yaso zaya yi, a wannan ranar da rayuwa
Inka mutu ayi maka kuka, idanu suyi ta zuban ruwa
Idanu suyi ta zuban ruwa, suyi ta zuban ruwa
Duk soyayyar ka da dangi ranar ta kare a gare ka
Bayan anyi maka waka, zaka ga ana ta saurin kaika
Yan'uwa abokan arzki zasu kaika cikin kabarin ka
A sanya ice a saman ka, sannan kasa ta biyo bayan ka
Wadan da suke kaunar ka su zasu yo addu'a a gare ka
Su juya suyi tafiyar su, a cikin kabarin ka su barka
Daga nan sai halayyar ka, ina kayi mai kyau jindadin ka
In kayi mara kyau halin ka, rannan ba mai kwacen ka
Ba mai ceton ka, ranan ba mai ceton ka
Kabari ranan ganina dashi na kasa bacci
Gabana sai faduwa yake, na kasa cin abinci
Ba zama ciki ba'a juyi, kwanciyar ciki irin na bacci
Tsawo, fadi daidai da kai babu kari domin karamci
Sannan ba hanyar iska da zata zo maka kamar mafici
A cikin kabari da bayani ba ankai ka bane kayi barci
Mala'iku zasu zo da su'ali, tambayoyi babu ragwanci
Ba sani kuma ba sabo, in kayi daidai ka samu karamci
In ka saba Allah a duniya daga nan ka fada kunci
Ka fada kunci, daga nan ka fada kunci
Yan'uwan ka sun manta ka, basa tuna ka a rayuwa
Aiyukan da kayo masu kyau, su zasu zame maka garkuwa
Da su za'a dinga tuna ka, jindadi ne gun yan'uwa
Har a dinga yi maka addu'a, sunan ka baza'ayi mantuwa
Wanda yayi aiki mara kyau mutuwar sa ba mai damuwa
Kaji wadansu na ta fadi an rage mugun iri a rayuwa
Ina amfanin mummunan shaida duba mini yan'uwa
Allah taimkaa mini, lahira kar in shiga damuwa
Kar in shiga damuwa, lahira kar in shiga damuwa
Idanu na ta hawaye na tuna ran tsayuwa a gaban gwani
Ranar tonon silili komai ka aikata sai ka gani
Sharri ko alkhairi ranan mutane duk sai sun gani
Sirrin da kayo shi cikin duhu (ranar jama'a sai sun gani)
Malaman da suke rufe gaskiya (ranar jama'a sai sun gani)
Da watan azumi ka sha ruwa (ranar jama'a sai sun gani)
Kai asiri ka kashe dan'uwa (ranar jama'a sai sun gani)
Ka cinye hakkin marayu (ranar jama'a sai sun gani)
Mai tauye mudi gun awo (ranar jama'a sai sun gani)
Ga zina anyi ta a boye (ranar jama'a sai sun gani)
In fashi da makami shi kayi (ranar jama'a sai sun gani)
Idan fashi da makami shi kayi (ranar jama'a sai sun gani)
Maza da suke neman maza (ranar jama'a sai sun gani)
Mata da suke neman mata (ranar jama'a sai sun gani)
Ka kashe rai kuma ka sha jini (ranar jama'a sai sun gani)
Anyo zabe kayi murdiya (ranar jama'a sai sun gani)
Mai shirka baka da gaskiya (ranar jama'a sai sun gani)
Shirka babban sabo ne dubiya (ranar jama'a sai sun gani)
Mace mai daga sauti kan miji (ranar jama'a sai sun gani)
Wata ta fita babu sanin miji (ranar jama'a sai sun gani)
Kudin cefane wata ta rage (ranar jama'a sai sun gani)
Mace mai cutar da kishiya (ranar jama'a sai sun gani)
Ta bada kanta ga boka (ranar jama'a sai sun gani)
Tasa magani a abinci (ranar jama'a sai sun gani)
Um, wayyo Allah (ranar jama'a sai sun gani)
Wayyo Allah yau tuba nake (ranar jama'a sai sun gani)
Ni Umar tuba nake Allah

Поcмотреть все песни артиста

Other albums by the artist

Similar artists