Ni maraya ne Ni maraya ne ♪ Iye amarya soyayya ango kaima soyayya Auren an daura dangi kowa na murna iye Da sunan Allah sarki zana faro waka ta Ahadun babban sarki kai ka kagi halitata Kai kayo mu maza mata sanan kace muyi ma bauta Aure na nan a ciki dangina fa mu inganta Yau ga wasu sun shirya rabbi zasuyi ma bauta Domin su na shirya ta Zana rero wakata Zanyi gyran murya ta uhm uhm idanyi nasiha ta Amarya kyakkyawa sarauniya ce tayo kwaliyya Ke kowa ke kallo yanata jiran takunki da dai daya Iye amarya soyayya ango kaima soyayya Auren an daura dangi kowa na murna iye Taro nan yayai taro maza da mata duka sun taru Ga iyaye ga yaye har kanne duka sun jeru Ga abokai harda kawaye nata jiran mai zai faru Kalaman bakina kowa ke yin sauraro Fatan da nake zancen da zanyi kowa ya karu Wasu sun dage da rawa wasu sun zauna a kujeru Maza taso ango ga amarya kaine jigo Babu kwanan shago tunda tasai ma bargo Amarya soyayya ango kaima soyayya Auren an daura dangi kowa na murna iye Eh hakuri jari ne ango da amarya kunjiya Hakuri riba ne ku gwada karshe kuci muriya Hakuri tsani ne ku rike shi da karfi igiya A zaman mu na duniya kar mu biyewa zuciya Ku zauna lafiya dan Allah babu hayaniya Dan wata rana zaku zamo iyaye bai daya Ina da yakinin zakuyai wa 'ya'ya tarbiya Ku tausasa zuciya dan Allah sai kuyi juriya Sai kuyi juriya hakuri sai kuyo juriya Amarya soyayya ango kaima soyayya Auren an daura dangi kowa na murna iye Kin dace da miji amarya zabin Allah ne Tinda anyima shaidar shi mai tsoron Allah ne Mai irin wanan hali ai zaya kare hakki ne Nasan zai baki kulawa zai rike ki amana ne A tsakanin juna ku zamo masu boye sirri ne Naji anyo shaidar ki amarya ina dada jan kune Naji ance zakayi ladabi da biyaya ga ango ne Dan ance kin iya girki sanan ga tsabta ne Kyauta daga Allah ne Kyauta daga Allah ne Amarya soyayya ango kaima soyayya Auren an daura dangi kowa na murna iye