Tankade da-da sai da rariya Rariya-rariya Rariya-rariya Rariya-rariya Tankade nayo na sa rariya Kece kika zam tsaba zabi na a soyayya Tankade nayo na sa rariya Kai ne ka zamo tsaba zabi na a soyayya ♪ Na takande soyayya ta na sa rariya-rariya Dan in guji cuta Allah ne mai kariya-kariya Kuma na dace dan na samo mai tarbiya-tarbiya Lafazin ta da dadi sam-sam bata ashariya-ashariya Nazam' gwanin so dolle ayi mini jiniya In na taho kiyo dauki ki min tarba ta soyayya Rariya-rariya ♪ Nayi nisa a so nai kololuwa loluwa Cikin kala damin nan nai yo tsuntuwa-tsuntuwa Kai ka zamai mini allura na cikin ruwa, cikin ruwa Nazama mai sa'a samun ka a rayuwa, rayuwa Duniya ta yau ta dawo sabuwa Kai ka shigo kayo aiki dolle in maka sakaya Rariya-rariya ♪ Ruwan sama in kaga yayi zubowa ai damina ce Aure in kaga yai daurewa wannnan kauna ce Cutar Allah na da yawa naga Baiwa-baiwa ce Shi ya hada mu dake kan aura an ce mun dace Na rasa ki a soyayya sai na mace Ko-ko jiki ya bar aiki tunda rabin shi ya tsaya Rariya-rariya ♪ A haggu da dama kai na gano kai Na fada wa iyayye, "Kai ne zabi" Littafin so ciki babi-babi Sunan ka yana ciki fannin hubbi Kowa kagani a cikin littafin gallery Dolle hannun sa 'kwai mulki koko sarautar soyayya Tankade nayo na sa rariya Kece kika zam tsaba zabi na a soyayya ♪ Tankade nayo na sa rariya Kai ne ka zamo tsaba zabi na a soyayya Tankade nayo na sa rariya Kece kika zam tsaba zabi na a soyayya