A zauna wataran a saba tilas ne Ki sanya a ranki arashi sai ya faru A zauna wataran a saba tilas ne Ka sanya a ranka arashi sai ya faru ♪ Soyayya ke na baiwa dukan kaina Hakika babu laulayi kin zauna 'Yan mata karda ma ku rabo guna Ba sauran gurin da zana baku ku zauna A raina ke kadai nasa kin kayi kwance Ki huta babu wanda zai zo sashin ki ♪ A neman lafiya ake allura Matso nan sahibi inyi maka hira A gefen farin wata za kaga zahra Mai neman wasan wuta jeka makera Soyayya ko ga gidan ta nan dan saurara Gwanaye mun zamo ba mai ce mana baki ♪ Nayi na'am dake a so zo zabi na Kina na nan ta ko'ina cikin labari na Zan nuna ki babu fargaba gun dangi na Su sa albarka a kan mu shine burina Diya ta gun ki zata ce miki Ummi-na Da aure zamu haihu in bada sadaki A zauna wataran a saba tilas ne Ka sanya a ranka arashi sai ya faru ♪ Na bayyana komai dake a raina Labarin Gizo-Koki ka ji kauna Cikin rai nayi ma guri ka zauna Kana sani farin ciki da murna Nima zanyi iya kacin iyawa ta kauna Na saka maka yanda kayi min ba baki ♪ Nayi shiga duba kice mini dan gaye Ke na rika karda kiyi mini tawaye Munyi kama mun zam tamkar tagwaye Ina dake a so na zarce hawaye Rabo na bai wuce ni tunda ina raye An daura aure na dake shi nafi dauki ♪ Ko anyi gasa, ni zan zama ta daya Babu wasa, kuma babu murdiya Mai ya kunsa, wasa ne da dariya Zo ka kwaso, soyayya Gasar so da za'a sanya mu zamu lasa Da murna mu dauki kambu muje muyi biki A zauna wataran a saba tilas ne Ka sanya a ranka arashi sai ya faru