Mai kauna ta ba wacce ta kai ki gare ni fannin so Kece farko, karshe a labarina soyayya Mai kauna ta ba wanda ya kai ka gare ni fannin so Kaine farko, karshe a labarina soyayya ♪ Mun girma, ni da ke a cikin so mun kayo sabo Akwai dama, auren mu da ke ashe inda rai da rabo Na soma mutuwa ta zamo rabuwar mu zo dibo Ki daina fushi Dukkan mai rai tilas yabar duniya Mai kauna ta ba wanda ya kai ka gare ni fannin so Nayi kuka domin watarana nasan sai mun rabe Matar ka zan kare mutunci naka kar ya zube Mai hauka ita zata rike shi a hannu har ya kadai Fatana mu kasance tare a sabuwar duniya Mai kauna ta ba wacce ta kai ki gare ni fannin so Kece farko, karshe a labarina soyayya ♪ Kaine kofar zuciyata duk wanda yazo kai zai iske Don haka ba wani mai shigan ta sai ka bashi dama haka yake Kaine mai mulkin ta, sarautar tawa kai ka rike Tawa daban soyayya ta a gare ka gangariya ♪ Tunda kin bani dama Ba zanyi wasa dashi ba A son ki zan zama kurma Sukar ki bazan jiyo ba Ba abinda zai sani nadama Zabin ki banyi kuskure ba In na dauko keke na kece zaki hau carrier Mai kauna ta ba wanda ya kai ka gare ni fannin so Kaine farko, karshe a labarina soyayya Mai kauna ta ba wacce ta kai ki gare ni fannin so Farko, karshe, labarin soyayya