Kalaman bakina saurara ki jiya yan mata Ya sunan ki? Don Allah daure ki fada in kin ji ♪ Farko nayi sallama zan so ki amsa min yan mata Matsayin ki musulma ai kinga hakan shine cancanta Gaki kyakkyawa ke surar ki ga kowa ba ta misalta Karambani nayi mutum ce ko aljan yan mata Ki min uzuri na tare ki a hanya zan yada manufa ta Ba son raina haka ya kasance karda kiyi mini rata In kika wuce bansan ina zamu gana ba kin kufta Shine sanadi na tare ki kan hanya ban shiryo ba ♪ Ko kurma ce ke tun dazu ina magana kinyi shiru Dalili ya kawo ni kinga hakan na zam kuturu Na rike kokon bara taimaka ki zuba mini koda gurguru Kiyi min magana inji sautin muryar ki Umar shi na biyo ♪ Ki tsaya kiji ni dai soyayya ce a gare ki na miko Na kwashe komai na cikin zuciya ta zamto konko Da zaki amince sai na tura iyaye na muyo baiko Domin ki sani gaskiya ta daya na rike ta tun farko Zan so ki guda hali na Ki aminta da duk kalamai na Nayi alkawari dare rana Ba zana saka ki kuka ba ♪ Bude kunni sosai yanzu in fada maka sunana Ammah kafin nan zan baka kadan daga labari na A Suleja nake nazo Kaduna ziyarar yan'uwa guna Kuma zan koma babu jimawa in na kare hutu na Soyayyah ya zata kasance mana idan ka auna Gari na masoyi baya nisa zan iya bin ki har Ghana Sunana Sunana, "Maryama-Maryama-Maryama" Kuma na yarje zan yi soyayya daga baki har zuci ♪ Nagode Allah da yasa kika yarda dani a soyayya Mai zan baki matsayin tukwici sai ki fadi na shirya Yaba kyuta tukwici na zance na ba karya Biyo ni muje gidan mu koda baka shiryo ba