Daga kallo daya na gane a soyayya mun dace Akwai biduri auren mu dake don na shirya Daga kallo daya na gane a soyayya mun dace Akwai biduri auren mu dakai don na shirya ♪ Na nema an bani wannan girma ne Burin rai samun shi jindadi ne Auren so sunnah shi aikin lada ne Ni da ke akwai shi masu matsayi ne Auren soyayya Mu kayo niyya Ba jayayya Muka daidaita ♪ Cancanta in an duba ba'a jira Halayya da dabi'u naka na ankara Nasan in munyo aure sai na shahara Jindadi da walwala kauna za'ayi bara Duk inda na tunkara Bani da tsara Komai na tara a soyayya Daga kallo daya na gane a soyayya mun dace Akwai biduri auren mu dake don na shirya ♪ Daga kallo daya na gane a soyayya mun dace Akwai biduri auren mu dakai don na shirya Kin zama, kin zama tamkar zinare zani kula ki Can ciki, can ciki karshe a cikin zuciyata za ni saka ki Ban bari, ban bari, ban bari, ban yarje ba ko kuda kar ya taba ki Don nayi yawo a kasashe Ban yo gamo da irin kyakkyawan fuskar ki Da iri na jiki Lafuzan bakin ki Su sani jiri ♪ Zo mu zauna nayi ma maraba Wuya da dadi bazan guje ba Yan gulma da suka bazan biye ba Duk wanda ya koce ka ya nemi gaba Don ina kishi Zan sanyo mashi Ko harsashi in buge makiyi na Daga kallo daya na gane a soyayya mun dace Akwai biduri auren mu dake don na shirya