Numfashi fita yake, ba adadi Rayuwa sai dashi ba madadi Yau kece madadi Ko ince sanadi Yau kece madadi Ko ince sanadi In bake ba batun Soyayya, zo muyo soyayyah ni dake Soyayya, don ko shine sinadari na zaman aure Soyayya, zo muyo soyayyah ni dake Soyayya, don ko shine sinadari na zaman aure ♪ Cikin zuciya tawa, tana yin bugawa Ga dukkan alamu kaine kake yin tahowa ♪ Cikin zuciya tawa, tana yin bugawa Ga dukkan alamu kaine kake yin tahowa Maza zo da sauri, muje shakatawa Kaban so in baka, muyo adana Gare ni komai kike bukata Zan yi miki shi cikin hanzarta Domin zuciyar ki in faranta A aikace ko cikin bayani Zuciya ka zagaye Ko'ina ka mamaye Zuciya ka zagaye Ko'ina ka mamaye In ba kai ba batun Soyayya, zo muyo soyayyah ni da kai Soyayya, don ko shine sinadari na zaman aure Soyayya, zo muyo soyayyah ni da kai Soyayya, don ko shine sinadari na zaman aure ♪ Fadin gaskiya tare shi ake kira so Tausayi da kyautatawa duk yana cikin so ♪ Fadin gaskiya tare shi ake kira so Tausayi da kyautatawa duk yana cikin so Kowa yana da wacce yake so Nidai ke nake so Ke dai zani furtawa so so Soyayya abar so Zuciya ka zagaye Ko'ina ka mamaye Zuciya ka zagaye Ko'ina ka mamaye In ba kai ba batun Soyayya, zo muyo soyayyah ni dake Soyayya, don ko shine sinadari na zaman aure