A makarantan nan duba ni na zama tauraro A zahiri ban daukan raini kar nayi juyayi Tayi ana yin shi a tsada ko kuma sari Karfin hannu kar ya tabo garwashi zai kona shi ♪ Idanuwa na sunyo hangen yan mata na tako Da dai, da dai-da ba jin tsoro sam-sam basa shakko Akwai guda dai a cikin matan mai halin yan tsirko Tana kira na kullum a waya bana amsawa Ta tura sakon text a waya ta sai nayi gogewa Ammah cikin makaranta shan kamshi kullum ne aikin ta ♪ Aji idan ya mace ta ja wannan ai dashi aka santa Ta kare mutuncin kanta kar yan yara-yara su biyo ta Ta canja fuska in taga alamun wajen ba tsaranta Ka nuna missed call a gani domin a gane ita ke kiran ka Ya zama shaida daga ranar ya zamo ka yanke son ka Jan aji zai kare nasan kowa zai gane ta ♪ Fadi na furta a tsakanin babba da yaro ke jan raini Nayi mata nisa ammah so take sai ta kamo ni In takaice zance na wuce da sanin ki a zamani Yan mata na gyaran zama da ido in sun ganni Shi abin sa'a ne bai guje wataran zaiyi dace Watakila na karba, watakila sai na tantance Tayi ana yin shi a tsada ko kuma sari Karfin hannu kar ya tabo garwashi zai kona shi ♪ A makarantan nan duba ni na zama tauraro A zahiri ban daukan raini kar nayi juyayi Abu mai kyawo na sai da kanshi ko ba talla Ruwa ba'ayi masa hanya ko'ina yaso zai bulla Dawisu idan ta fito tilas ne kowa zai kalla Idan anayin zancen ka, ka kai ka gode Allah Komai nake yi ido yana kaina Masha Allah A yanzu nasan na ci gari na kai labari ♪ Iya baki, kama bakin ki kar kiyi min raini Ka fadamin tilas na fada ma tunda kai ka tabo ni Shikenan zani wuce kar kiyi kuskure ki biyo ni Mota da jirgi hanya tasu ba zata hade ba A makarantan nan duba ni na zama tauraro A zahiri ban daukan raini kar nayi juyayi Tayi ana yin shi a tsada ko kuma sari Karfin hannu kar ya tabo garwashi zai kona shi