La-la-la. la-la-la Hmm, hmh So-so So-so Ni dake mun dace Kece kika ja Wayyo yau ya-ya za nayi? ♪ Na yarda dake ke na baiwa sirrin zuciya In zanyi sai dake rashin ki zai sa in sha wuya Allah ya bani ke, na cika buri na zuciya Ruwan idaniya na kece mai sa su kwanciya ♪ Koda magani, soyayya ba zana barki ba Ko an razani, domin ke ba zana ji shi ba Ko baturiya, in tazo bazan kalle ta ba So na gaskiya, kin nunan dai-dai da zuciya ♪ Ina alfahari soyayya ba za'a fini ba Yau naci gari a zato na bazan rasa ki ba Ina da damuwa ammah na barwa zuciya Ruwan idanuwa na waye zai su kwanciya ♪ Soyayya dace ne Cika buri jindadi ne Sanin sirri don yarda ne In kin furta min dai-dai ne Kisa a ranki za'a baki wanda kike so In biya sadaki a kaiki daki na da kike so Zani baki dukka hakki auren mu na so Kowa na fadin dani dake mun dace So-so So-so Ni dake mun dace Kece kika ja Wayyo yau ya-ya za nayi? Soyayya ashe tana zafi Zafin ta ya zarce garwashi dafi Tamkar rijiya take a cikin ta akwai zurfi Ciki na fada ina bukatar tallafi