Ga bako yazo gun ki Soyayya ce zan baki Soyayya Albishiri na dauko a ina zan sauke zuciyata don isar da sako Kofar soyayya na kwankwasa, wacece zata zo karbi sako Albishiri soyayya linzami ce ta jani korama a can na hadu da bako A rayuwa zuciya sai da makwabci, wanda zai sa zuciya tayi karko Albishiri na yarda da soyayyar ka, nayi masauki a zuciya gare ka bako Bako mai kyawun sura ba da kamala, burin zuciya ta mallake ka bako ♪ Sura na zuciya dai zane, sako ne ko baki duba ba Murmushin da nayi in kin duba sako ne ko baki gane ba Sa'ilin da nace kece tauraruwar mata, sako ne in baki manta ba Fure na baki daure ki karba, karki ce a'ah sako daga ba Albishiri soyayya linzami ce ta jani korama a can na hadu da bako Kofar soyayya na kwankwasa, wacece zata zo karbi sako Har kullum in zana gan ka idanuwa ba zasu zubda hawaye ba Inko har zan ji sautin muryar ka kunnuwa basa kurmance ba Inko har naji kamshi na jikin ka, zuciya ba tayo kuna ba Da sannu zuciya take yin masauki, tayi lale da marhaba da zuwan bako Albishiri na dauko a ina zan sauke zuciyata don isar da sako Bako mai kyawun sura ba da kamala, burin zuciya ta mallake ka bako Raina a gare ki fansa ne, na sadaukar gare ki ba laifi ne ba Inhar zanyi hawaye domin kiyi murmushi, lalle na sani banyi asara ba In har zanga fuskar ki duk second daya, har abada dake ba zana kosa ba Dube ni na taho dauke da sakon son ki, hannu na ina bara dauke da koko Albishiri soyayya linzami ce ta jani korama a can na hadu da bako Kofar soyayya na kwankwasa, wacece zata zo karbi sako Zuciya taka ce na baka masoyina, domin kai kadai ka dace da mafarkina Wataran na sani zaka zama aboki na, zama na har abada ka zama makwabci na Kamannin ki idanu ba zana manta ba, kin dace da malakar zuciya ke ta duba Karki yi nisa zuciya dake ta saba, kusanto ni zo ki tallafe ni bako Albishiri soyayya linzami ce ta jani korama a can na hadu da bako Kofar soyayya na kwankwasa, wacece zata zo karbi sako Albishiri na yarda da soyayyar ka, nayi masauki a zuciya gare ka bako Bako mai kyawun sura ba da kamala, burin zuciya ta mallake ka bako