Na sa a rai aure na sai dake yanmata Tunda kin amince min zuciyata babu sauran kuka Na sa a rai aure na sai da kai dan gata Tunda ka amince min zuciyata babu sauran kuka ♪ Bazan manta ran da idanuna sukaiyo gamo ba Bazan mance farkon haduwar zancen ki da kunnuwa na ba Ranar da kika sace zuciyata ba zana manta ba Nasa cikin kundin tarihi zan fadawa ya'ya na Na sa a rai aure na sai da kai dan gata Tunda kin amince min zuciyata babu sauran kuka Dama an fadi rabon kwado bai hawa sama ya zauna Koda ya haye tilas ne ya fado a kasa su gana Matar mutum kabarin sa ko yana Nigeria ita ko Ghana A sannu-sannu zaya zo su hade a kulla auren sunnah Na sa a rai aure na sai da ke yanmata Tunda ka amince min zuciyata babu sauran kuka Soyayyah na kulle dakin ta a kan ki na tsaya Bana so a san ma kofar ta, daga nesa a tsaya Ni da kaina nake yin gadin ta, na riko kibiya Sannan ban hada ki da kowa ranki banso yayo kuna Na sa a rai aure na sai da kai dan gata Tunda ka amince min zuciyata babu sauran kuka ♪ Na sa a rai aure na sai dake yanmata Tunda kin amince min zuciyata babu sauran kuka Dadi na soyayyah za'a fadi ba'a zarce ni ba Koda nida kai nace na fadi ba za'a karyata ba Idanun ku suma shaida ne ban san wuya ba Kaine ka saka ni cikin yanayi bazan so fita ba jigo na ♪ Dole mu gode Allah sarki da yayi nufin haduwar mu Arziki talauci shike yi ga wanda ya so cikin mu Ku muyi mar biyayya komai muke so shi zai bamu Sannan mu dau hakuri zamu ci riba dare koko rana