Bazan Barki Bah La-La Nima Bazan Barka Bah ♪ Na rike ki bazan barki bah Zani so mu zauna a rayuwa Ke na baiwa sirrin zuciya Ki rike ni amana kin jiya Na rike ka bazan barka bah Zani so mu zauna a rayuwa Kai na baiwa sirrin zuciya Ka rike ni amana ka jiya Zuciya, Jiki na ai naki neh Ke na baiwa komai kin sani Kin zamo ni, ni na zamake tun tuni Ba abin da ya rage koh kan kani Dukka sirrin da ke a cikin zuciya ta Na tattaro gare ki zan zayyana Dukka sirrrin da ke a cikin zuciya ta Na tattaro gare ka zan zayyana Na rike ki bazan barki bah Zani so mu zauna a rayuwa Haduwar da mukayo nida kai Soyayya muka kulla kan gaskiya Zuciya ta tayi na'am Rayuwata da kai zan zauna duniya Dan hallayar ka bani da fargaba A dalillin masoyii na ban jiya Kan hallayar ki bani da fargaba Zan zamo adali a gwan ki Sa'ar zuciya Na rike ka bazan barka bah Zani so mu zauna a rayuwa ♪ Na rike ki bazan barki bah Ka rike ni amana ka jiya Ya-yafi ya sauka gari yayi sanyi Da bargo na sanki na rufe jikina Rana daya in har bangankaba sai nai juyaya Na saka ka a rai dan Allah kar ka sani rana A cikin zuciya ta ke che mai yayi Abandan bani so ranki ya zamma mai bako na Zo kayi mani tinani Babu Karya A cikin su Malami neh kai na samari ♪ Babban farinciki na a daura mani aure Mu zauna a daki, dani da ke a tare Rana daya zanyi ma kwalliya irin ta amare In zana lallai a jikina In fesa turare Daga ranar na bar damuwa Tunanni ya kare Na zama na ina gannin ki Lallai na morai Sanki ya fitti nai ni Ya hana ni sukuni Shinn, ina zaki kai ni Masoyiya ta Na rike ka bazan barka bah Zani so mu zauna a rayuwa Ke na baiwa sirrin zuciya Ki rike ni amana kin jiya