Wani gari Wani gari Wani garin da ake kurba man gyada zalla Wani gari Bai kai gabas ga nisa ba Wani gari Bai canja a suna ba Wani gari Bai kai arewa hali ba Wani garin da ake kurba man gyada zalla ♪ Wani garin da ake kurba man gyada zalla A wani garin sun tashi basu cin tata Duk ayukan su sai ilimin ka, ka kyauta A wani gari rana take bidar danta Cikin sarautun su ko basu duba kankanta A wani gari nema yakan zama sata Suna da gona kuma basu kyauta noman ta A wani gari mata suke fita tsinta Tunda masu kudi basu san su dan kyauta Wani gari ne ba dan isa da kudi ba Wani gari ne ba a san fita da kaya ba Wani gari ne basu fidda kai da zakka ba Wani gari ake kurba man gyada zalla Wani gari Bai kai gabas ga nisa ba Wani gari Bai canja a suna ba Wani gari Bai kai arewa hali ba Wani garin da ake kurba man gyada zalla Rayuwar wani attajiri na dauko Rayuwar wani hamshiki yau na leko Akwai kudi sai dai masu saka mutum tarko Dan ko ya tara ba shi cinsu yai tarko 'Kwai ilimi ga 'ya'ya gare a duk sako Duk inda yaje aure yake kamar mako Matan sa shidda ne kaga ya wuce iya kako Jahili ne gashi ba sani furen sobo Wani gari zai aure sai ya bar 'ya'ya A wani gari Zai tara dan karen kaya A wani gari Zai so magi ya bar saura A wani gari Mai binna dukiya zalla Wani gari Bai kai gabas ga nisa ba Wani gari Bai canja a suna ba Wani gari Bai kai arewa hali ba Wani garin da ake kurba man gyada zalla Ana kwana ana kwana ana tashi (toh fah!) Yana tare da 'ya'yan da suka ki tashi (umm-umm) Suna san su fantama da dukiyar shi (umm-umm) A cikin 'ya'yan da akwai guda daban shi (umm) Yana nan yana nan yana karatun shi (umm) Yana nan da ilimi da hankali na shi (umm) In mutunen ya karkace sai ya jawo shi (umm) Yana bashi tallafi cikin karatun shi (umm) Amman mutumin baza shi karba ba Ba zai zamo a cikin masu fidda zakka ba Ba zaiyi komai domin ya gyara bauta ba Muten gari baza ma su more komai ba Wani gari Bai kai gabas ga nisa ba Wani gari Bai canja a suna ba Wani gari Bai kai arewa hali ba Wani garin da ake kurba man gyada zalla Bari kuji, bari kuji, bari kuji, bari kuji Allahuma Da'da mai tarbiya da dadi (umhum) Koda duniya da zafi (tabbas) Neman lahira da dadi Koda tai hadi da kaifi Bari kuji, bari kuji, bari kuji, bari kuji Allahuma Rana ta fito da zafi Malam ta raba duniya da kudi (ah-ah) 'Ya'yen nasa sun ka zauna Sunyi shawara ta zauna Akan kawar da shi daga duniyar Ko zasu zauna akan dukiyar sa Bukatun su suka auna Domin mutum ne shi ba dai isa da kudi Wani gari Bai kai gabas ga nisa ba Wani gari Bai canja a suna ba Wani gari Bai kai arewa hali ba Wani garin da ake kurba man gyada zalla Sun kar shi an shiga uku sun kar shi Sun kar shi an shiga uku sun kar shi Ba mutuwar sa ba akwai wani harsashi Mata shidda ya da'da a iyakar shi Ga kowa yana bukatar dukiyar shi Daman baya basu yunwa a gidan shi Ga kagara kaga duk sun hau nishi Kowa yana kiran shi ne dan shi Shi ne dan shi, shi sai an bashi Ya tara dukiya zalla Aure yake ya bar 'ya'ya Ya binne dukiya zalla Sun kar shi Sun kar shi Sun kar shi Ah-ah-ah-ah, mun shiga uku sun kar shi
Ayi adalci Ayi adalci Ayi adalci ♪ Allah yasa mu dace Allah shi bamu ikon gyara ibadun mu