Yee Yanda kunne yaji haka zuciya ke aunawa Inda raina da rabona zakiyi gane wa Nida ke sirrin juna zamuyi boye wa Ra'ayi na kece kika zamto tawa Ki kula min da kaina ma'ajin sirri na Haka shine zai sanyaya ruhina Wa'adina yazo indai baki sona Tunda naji wayansu a kanki suke zagi na Kinga toh na san ba'ayi saida hakora Ki kira ni a gefenki nazo na sarara Ko a dan aiki dauke ni na kore kura Nifa ba komai kanki kada amin kyara Ni kawai sonki nake dan zuciya ta harbu Da ace zakiyi shagwaba ni zan miki bambu Fadamar sanyi kika so na hada miki lambu Kanki zan iya danne ko da hannu ba kanbu Tausaya min agaza min kada kiyi min bore Na aiko sakon nin so karda ki share Inna rasa ki masoyiyata dole na zare Shi dafin so naki da wuya taya zan jure Kalmomin da kike min nake yin hadda A kwakwalwa ta na ajiye su zaman min shaida Bani in baka so ne baya yin tsada Nayi sabo dake son ki zuciya ya huda Ki tuna ni dake kowa tare ya ganmu Hanta da jini tilas sai an barmu Nayi kuka kwakwalwa sonki yake damu Na zarina aure nake ataya zan samu Babu laifi dan ni ke daya nayi wa kishi Ko kallon ki naga wani ya nayi sai na tsane shi So ya danne ni a sa'in da kyar za nayi nishi Kinji sako na ina fatan da ki karbe shi Kada ki bari ya zamana kuka Ni masoyine kanki kaman nayi hauka Ki gina min sharudai naki kawai na dauka Dan kaunar ki nake babu dare ba rana A jikina nake ji kina saurare na A bar kauna ta kin tsaurara alwashina Babbakar ruhi kaunar ki tana ta guda na Kanki de na zaku daure ki zamo gatana Inna fatan wataran ki kirani habibi Zanji dadi mai sona ko bayan rai na Ko da ace a duniya ba numfashi na Kin tuna wanda kike so ya zamo ni dai na