Kauna garkuwan jiki naki ya taba ni Kece farin cikin raina-raina Kauna garkuwan jiki naki ya taba ni Kaine farin cikin raina-raina ♪ So rayuwa ne wanda ke gini Naki kin ka bani ya zamo sani Zuciya da ruhi can kikayi rini Ba kamar ki tabbas naji na gani So ruwan zuma ne, kinyi min tuni ne Zani baki yarda keko ki bani kauna ♪ Nayi farin ciki da soyayyah In na gan ka har ina kunya Karka barni za nayo jinya Makiya mu sasu suyi kunya Kai ka bani kauna nayi farin ciki Rayuwar mu ta kasan ce da martaba ♪ Yadda kikayi mini nagodewa Kaunar da nake maka nayi ninkawa Shine sirrin da nake boyewa Koda baka furta ba ina ganewa Indai kika ce min "kule" zan cashewa Za muyi gasa aga mai sarewa Aikuwa ki shirya wa kafan tserewa A gani a kasa tunda muna nan gamu ♪ Babu kamar ki duk cikin duniya Koda ganin ki doguwar yarinya Zama dake kawai na shirya Kyawun halin ki gaki mai tarbiyya Mai farin idanu Nayi ta jiran ki sannu Zuciyar ki tawa ce ai dole in kulawa Dole nayi kulawa ♪ Kayi kirana na amsa masoyina Son ka yake mini yawo a kirji na Ko kiya ma na ganka a barci na Nayi ta fadin sunan ka a baki na Wata ta rabe ka akwai kuna Ni daya ce ba kari da mun aure Kauna garkuwan jiki naki ya taba ni Kece farin cikin raina-raina