Amana da amana da aminci Idan so yakai so da karamci Kisani sahun farko inyi wakilci A zuciya in dauko soyayya ♪ Ina da idanu bazanki na kalla ba Masoyi na gaske bazai ki masoyi ba Na mallaki baki ya bazan saki zance ba Ki soni kawai tunda zuci ke tayiwa lamba Jiya nayi mafarki Gunki na zama sarki Kinyi mini alkairi da zuciya kin bani Idan da bukata aikenki ki aike ni Zanyi miki gata tunda sanki ya raine ni In zan tina baya wai a kanki a kere ni Amfanin hakuri gashi ni na ciyo riba ♪ Kece kika soni kin bar mini bashi Kyawu fa akwai shi sai ma kin baza gashi In dai kika barni tillas nayi toshi Ina da bukatar nayi aure Indai nashigo zan rufe kyaure Ya zama halali akanki nayo kishi Wakarki nake yi zo kiyi mini amshi Kar so ya kasance tsuntsu mai tashi Kece na rike zan saki kowa Rashin ki kawai zanayi kewa Dake zan zauna daram dam da amana ♪ So ya zama kauna ki gane nufi na Kaunarki nake yi nasaki a raina Dake nayi yarda ki mallaki kaina Jiki da jini so kin dada raina Na baki guri fada zo shiga ki zauna Gatan so yarda kinzo karni na Ina miki zance kina dubi na Madubin dubawa na dubin fuska na Ina jin ki a raina kice zabi na Yarda da aminci sune soyayya