Kishore Kumar Hits

Auta mg boy - Zuciya Ta lyrics

Artist: Auta mg boy

album: Zuciya Ta


A mg boy record
Abun da nai nema a gunki na sama
Ban fita ba nima sai da hutata
Ki gyra dankwalinki ya kalli fuskata
Kana da hula kaima sai ka setata
Babu mamaki so ba'a mai wauta
Gareka yau nima na baje hajata
Zuciyata ta aminci sai dake zatayai zama
Wanda kaso shi ya soka, ku ji dadin rayuwa
Nima zuciyata ta aminci sai dakai zatayai zama
Wanda ya soka, ka so shi, kuji dadin rayuwa
Sanki nake nema, zaki amince mun
Karki butulce mun, ki ki karba ta
Kai na fito nema, har na amince ma
Kar kaji ba dadi, zanayi ma gata
Tunda kina so na, zo ki ji zance na
Baki zama rana, autar mata
Ban ga dalili ba, ban rasa huja ba, ban yi asara ba in nayi ma bauta
Naji ana cewa na fiye gagawa, sanki yake sawa in sake hanya ta
Komai suka ce bar su, soyayya ce, komai kayo kaina tabbas ka kauta
Sanki nei, har ya ja ni
Ni dake, kwai bayyani
Rai da buri, karki bar ni
Sanki na hauhawa donko babu tsani
Ina dake, na wuce raini
A zuciya take a ganmu abar mu
Amfanin nema rabonka ka samo
In ka dawo gida furarka na damo
Sanka a raina yana gudu kamar zomo
Yadda nake jinka ko na tafi zan komo
Ba mafarki ba, ba tinani ba
Sanka a zahiri nakeyin sa in kaji

Поcмотреть все песни артиста

Other albums by the artist

Similar artists