Masoyiyata kizo muje, mu zagaya, ko garin da ba kowa Masoyina zan so kazo muje, mu zagaya, ko garin da ba kowa Sai kazo muje Koh garin da ba kowa Nidai a zuciya, ke na aiyana Na baki so, sai ki bayyana Kin zama bango dake na jingina Kece rigiya daure ki bani ko ruwa Zuciyata da kaunar ka nei tai girma Bani yarda akan sanka ai banmarma Na dade a kaunarka nazama kurma Ka bani yardar ka zata sa inyi rawa Da fili da boye, zan miki soyayya Dubi idanuna, cikinsu akwai kunya Koh daga ni ma, ka cika 'da mai tarbiya Koh ba'a fada ba, nasan ka iya soyayya Koh a kalamai, gareki na kan koya Auren mu dake za'ai domin kuwah na shirya Kazama madubi na Kin zama ruwan sha na Kazo a mafarkina, bacci yayai min kawa Ya zanayi, in babu ke Raina da zuciya, kin mallake Kin zama ni, na zama ke Gida daya, mu zauna dani da ke Masoyiya, kar mu farake Rashin ki zai sa in dinga jinjuwa Sannu jarumi na ko nace dakai jarmai Gida da daji kai na bar ma duk komai Akanka na yarda a kirani ma komai Duk wanda zai ja dakai a zuciya naramai A bani kai, ni yafi mini ma komai In dai dakai a duniyar ga ban ganin kowa