Kishore Kumar Hits

Salim Smart - Linzamina lyrics

Artist: Salim Smart

album: Linzamina


Linzami na
Soyayyah ce kuma ta jani
Ta tafi dani
Ban san ranar dawowa ta ba
A tunani na
So inzai shiga zaiyi bayani
Neman izini
Gun wanda yake san kamawa
Yan mata bar cika baki
So baya yin zabi
Bai duban wani kyawunki
Ko kuma sura da zubi
Ke dai rike addu'ar ki
Sannan ki barwa Allah yabi
Jiki da jini
Soyayyah ba ranar daina wa

Mai kushe so ka daina
Asalin ka ne, kar manta
Gare mu so yayi rana
Sanadin shi ne muka huta
Allah yana yafe mana
Don son fiyayyen halitta
Albarkacin so yana nan
A fassara ya wuce nan
Ya zan na manta da wannan
Kalmar da kinka fada min
Dadin ta yayi mini kawa

Habibi na
Mai kishi na
Kuma jagora na
Mahadin rai na
Amini na
Kuma ruhi na
Ma'ajin sirrina
Mai milki na
Kai dai zanyi wa kirarin soyayyah
Inyi maka take
Komai kace inyi ba wata jayyaya
Zanyi shi a take
Bana gudun a kirani da mai jinya
Akan so na kai
Koluluwa a rashi naka na shirya
In zama gawa

Nima ina kaunar ki
Daga zuciya har baki na
Kullum ina kewar ki
In bake a kusa nufi na
Ke dai kike yin mulki
Daga ke ba wata a raina
Koda kiran sunan ki
A kayi sai inji na shiga murna
Linzami na, ki rike mini jari
Yarda bani, ki ciren radadi

Поcмотреть все песни артиста

Other albums by the artist

Similar artists