Ahh, ba kowa zai gane ba Yanda ake jin zugi Indai har so ya darsu koh kuma yai maka barna Ni kam so yai min barna Ya chanja min suffana Ya mai san tamkar bare a cikin dangina Ya sauyan lissafina Ya tauye mini hakki na Yasa na baje sirrina ♪ Sumbatun soyayya, shin menene ke jawowa? Yaudara ce ko kuma kula? Ku ban amsata Amma wani sa'in zuciya ta ce ke harbawa In na tuna cewa a soyayya nayo bauta Wasu har sun chanja mini kallona Sun kasa su gano meke damuna Ni daya nasan menene ciwona Magani nasa Allah daya ne gata na ♪ Ehh, in na mutu kece sanadi Sannan kuma baki da madadi Samun wani mai kaunar ki kamar ni ba lallai ba Hanyar da kike so zana bi A silar so nai maki ladabi Amma haka bai sanya ki tunanin fasa butulci ba Menene soyayya inba karya ce ba Menene soyayya in ba cuta ce ba Menene soyayya inba hadari ce ba Na raina na huta harkarshen ra'ayi na ♪ Yaya zakiyi da hakkin soyayyata Kin saba mini da so kuma kin min keta Kin barni alaka tamu kin yanke ta Kin mamaye sashin zuciya kin chanja ta Ko wani laifi nayi maki ne? Ban roki ki yafemun ba Domin na horu da soyayyarki tun ban saba ba Yau kuka gobe kuka ni dai bazan jure ba Tunda Allah na nan addua ce zatayi gadi na