Ka dubi Allah ka tausaya ka daina yi min azaba da so Kasan akwai rauni tare da zuciyar da takamu da so Ba korafi nake maka ba Nuni nake maka akan haki na so Dani da kai yan uwa ne Sannan abokan juna ne Tunda dukkan mu musulmai ne Masu riko ne da addini Tunda ina san ka kagane hakan Toh kayi mini sassauci ♪ Idanwa na sunyo rufewa Ban gani bani ji a komai Hankalina yayi gushewa So yayi min dauri na gwarmai A sanka ni bani da dalili Koko hujjar fadar misali Zuciya kai ta ba muhali Taimaka min na sami yan ci ♪ Mi zanyi in sa ka farinciki Mine tunani na kasani Ina dakon so nike nufi Amman kamar ma baka gani In nayi maka kulawa Balantana ma kawo yabawa Gashi so ya zam jarabawa Garai ni ba damar nai gujewa Da zuciya daya nake ta san ka Karda ka sanya ni nai maraici ♪ Eh duk wasu sharude na so na cikin su'oi ka duba Na fi dukkan mata dake gurin nan aji da haiba Koda ban fada ba idan kana so zai shaida lamba Durkusa man har kasa ina ne ban maka ba Zuciya tai fes fes babu komai in ban sanka ba Ni babu ranar da zana ki ka Da kai nakeson samun kusanci ♪ Toh duk ku dakata Baza na so ku ba Bansan ya za ai na so ku ba So baza na yi shi ba Domin ko ban shirya masa ba Dalili na sirri ne Babu hali na zayyane Karku yi tunani ina sane Kukuma zan chi zarafin ku ne Hakuri ni shi zana baku Fata na kar ranku ya bacce ♪ Jinin da ke gudana a jiki na naka ne Walwala ta da murna dukka sanadi na san ka ne Ga zumar so ki kurba Sha ki bani Da hanu na ka karba Jani kai ni Numfashi na da naki Bugu dai suke Numfashi na da naka Bugu dai suke