Na kira ta, "Muradin zuciya" Abar kauna ce A garan ta zarce sarauniya Ita rabin rai na ce So yai mini bazata Ya shiga lokan zuciya Duk yayi dabaibaye a jiki har ya taba lafiya Dube ni ki gazgata Ke daya zan wa bibiya In na ambata ki yarda na zauna lafiya Idan da akwai rabo Aure zami ni da ke Koda basu so Allah shi zai bamu dama ♪ Hidima muke wa juna Soyayyar mu na da tsari Girma yake jiki na Da na hange ka ko a tari Fama ake da ni A kan kaunar ka na ci buri An ja naki saki Na na che zan maka bauta Baka tauye haki A so baka da mugunta Linzamin zuciya Rike shi ka mallaki rayuwa Ni na gaz gata kai daban a mazajen duniya A fannin so da so Ni dai kai zan baiwa girma ♪ Zuciya ta rufe da ke Babu abinda zai raba mu Aure in mukai da ke Babu wanda zai jikan mu Kyauta Allah ya ban ke Wasu so suke su samu So na zahiri da boye Ke dai nake wa nuni Shi so ya wuce wasa Gano ka rike ri rita Tun-tuni yai mini rasa Ya bi jini hanta ta